Ministar Tinubu Ta Sauya Sheƙa bayan Ta Shiga Gwamnati? Shugaban APGA Ya Yi Bayani
- Shugaban APGA na ƙasa, Sly Ezeokenwa ya yi karin haske kan jam'iyyar Bianca Ojukwu bayan ta karbi mukamin minista a gwamnatin Tinubu
- Ya ce har yanzu karamar ministar harkokin kasashen waje ƴar APGA ce, ba ta bar jam'iyyar ba bayan naɗa ta a muƙamin gwamnatin APC
- Ezeokenwa ya ce ya yi magana da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan naɗin Bianca kuma da izinin jam'iyyar APGA ta karɓi muƙamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban jam'iyyar APGA na ƙasa, Sly Ezeokenwa ya ce har yanzun Bianca Ojukwu cikakkiyar ƴan jam'iyyar adawa ce.
Mista Ezeokenwa ya ce duk da naɗin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi mata a matsayin minista, tana nan daram a matsayinta na yar jam'iyyar APGA.
Shugaban APGA ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirin siyasa a yau ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bianca Ojukwu ta zama ministar Tinubu
Bianca Ojukwu na daya daga cikin sababbin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya nada a lokacin da ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul a watan Oktoba.
Duk da cewa ba 'yar APC mai mulki ba ce, Tinubu ya nada matar marigayi Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu a matsayin ƙaramar ministar harkokin waje.
Shugaban APGA ya magantu kan naɗin Ojukwu
Da yake tsokaci kan lamarin, Ezeokenwa, wanda kotun koli ta tabbatar masa da shugabancin APGA, ya jaddada cewa Bianca Ojukwu ba ta fice daga APGA ba.
"Na kira shugaban kasa kuma na yaba masa a kan wannan nadin. Ita (Bianca) ‘yar jam’iyyar APGA ce, cikakkiyar mambar majalisar amintattu BoT ce har zuwa yau."
"Babu inda ta sanar da barin APGA, ta karɓi wannan muƙami ne a matsayin ƴar jam'iyyarmu," in jiEzeokenwa.
APGA ta amince da naɗin Bianca Ojukwu
Shugaban APGA ya ƙara da cewa cewa jam’iyyar ce ta ba Ojukwu izinin karɓar wannan muƙami na minista a gwamnatin Tinubu.
Ya ce abin da shugaba Tinubu ya yi kuma yake yawan kira da a rika yi shi ne jawo ƴan adawa a ba su muƙami a gwamnati mai ci, Daily Post ta ruwaito.
Shugaba Tinubu ya naɗa ɗan Abiola a muƙami
Ku na da labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya nada ɗan marigayi Moshood Abiola (MKO) muƙamin hadiminsa na musamman a gwamnatinsa
Mai girma Tinubu ya nada Jami'u Abiola a matsayin hadimi a bangaren yarurruka da harkokin kasashen waje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng