Gwamnoni Sun Taso Shugaban PDP na Kasa da NWC a Gaba kan Taron NEC

Gwamnoni Sun Taso Shugaban PDP na Kasa da NWC a Gaba kan Taron NEC

  • Gwamnonin PDP sun ba shugabannin jam'iyyar na ƙasa watanni uku su shirya taron kwamitin zartarwa watau NEC
  • Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa bayan taron da suka yi a Filato
  • Ya ce duba da abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar, ya kamata a shirya taron NEC domin ɗaukar matakan da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Gwamnonin jam'iyyar PDP sun tattake wuri kan taron kwamitin zartarwa (NEC) wanda aka sake ɗaga wa har sai baba ta gani.

Gwamnonin sun buƙaci kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin Umar Damagum ya kira taron NEC daga nan zuwa watan Fabrairu, 2025.

Gwamnonin PDP.
Gwamnonin PDP sun bukaci NWC ya shirya taron kwamitin zartarwa a farkon watan Fabrairu Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Kwamitin NWC ya ƙara ɗaga taron NEC

Daily Trust ta ruwaito cewa tun watan Agusta, NEC ke ci gaba da ɗaga taron kwamitin zartarwa wanda ake sa ran za a tattauna kan muhimnan batutuwan da suka shafi PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun shiga ganawa a Jos, sun jero tsare tsaren kawo sauyi a kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga ciki har da batun yadda za a naɗa sabon shugaban jam'iyya na kasa wanda zai maye gurbin mukaddashin shugaban PDP, Umar Damagum.

A watan Afrilu PDP ta sa taron NEC ranar 15 ga watan Agusta, ta daga zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, daga bisani ta kuma dagawa zuwa ranar 28 ga Nuwamba.

Haka zalika a wata sanarwa ranar Alhamis, sakataren PDP Samuel Anyanwu ya ce NWC ya sake ɗaga taron sai baba ta gani, Leadership ta ruwsito.

NEC: Gwamnonin PDP sun ba NWC watanni 3

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya ce:

"Mun amince da ɗaga taron NEC na baya-bayan nan saboda alhinin rasuwar matar abokin aikinmu, Gwamna Umo Eno, wadda za a birne a ranar da aka shirya taron."
"Bisa haka muna kira da babbar murya ga NWC ya kira taron NEC a karshen makon farko na watan Fabrairu, domin tattaunawa da neman shawara daga masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa ban miƙawa Ganduje shaidar cin zaɓena ba," Gwamnan Ondo ya kare kansa

PDP ta musanta dakatar da shugabanta

Kun ji cewa kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta kasa ya yi fatali da yunkurin dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Kuros Riba.

Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya ce a tanadin kundin tsarin mulki, kwamitin gudanarwa na jiha ba shi hurumin dakatar da shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262