"Dalilin da Ya Sa ban Miƙawa Ganduje Shaidar Cin Zaɓena ba," Gwamnan Ondo Ya Kare Kansa

"Dalilin da Ya Sa ban Miƙawa Ganduje Shaidar Cin Zaɓena ba," Gwamnan Ondo Ya Kare Kansa

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kare kansa kan rashin gabatar da shaidar lashe zaɓe ga shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje
  • An ruwaito cewa gwamnan bai bari Ganduje ya rike takardar shaidar lashe zaɓen da INEC ta ba shi ba a lokacin da ya ziyarci hedkwatar APC
  • Sai dai ya ce yana sani ya yi hakan saboda a tunaninsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ne mutum na farko da ya kamata ya gani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamnan Ondo, Lucjy Aiyedatiwa ya ce ba rashin mutuntawa ta sa ya ƙi nunawa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje shaidar lashe zaɓensa ba.

Aiyedatiwa, wanda ya samu nasara a zaben gwamnan Ondo ranar Asabar da ta gabata, ya karɓi takardar shaidar lashe zaɓ daga wurin INEC ranar Laraba.

Gwamna Aiyedatiwa da Ganduje.
Gwamnan Ondo ya ce shugaba Tinubu ya kamata ya fara nunawa shaidar nasarar da ya samu Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Bayan ya karbi shaidar a hedkwatar hukumar zaɓe ta kasa da ke Abuja, gwamnan ya jagoranci shugabannin APC na Ondo sun ziyarci kwamitin gudanarwa (NWC).

Kara karanta wannan

'Tinubu bai san ya aka yi ba': Ganduje ya fadi yadda suka yi nasara a zaben Ondo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje: Gwamnan Ondo ya ziyarci hedkwatar APC

Punch ta ce duk da tarbar da aka masu, Aiyedatiwa da mataimakinsa, Adelami Olaide ba su ba Ganduje satifiket na shaidar cin zaɓen ba kamar yadda aka saba.

Jim kaɗan bayan ganawa da NWC, gwamnan ya shaidawa manema labarai cewa da gangan ya ƙi damƙawa Ganduje takardar shaidar nasarar da ya samu.

A cewarsa, ya yi haka ne saboda a ganinnsa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne mutum na farko ya kamata ya fara miƙawa satifiket ɗin kafin kowa.

Zaɓaɓben gwamnan Ondo ya kare kansa

"Da farko dai ya kamata na gabatar da takardar shaidar cin zaɓe ga shugaban kasa, jagoran APC to amma kun san ba ya ƙasa."
"Wannan ya sa ban ba shugaban jam'iyya ba, ba wai rashin mutuntawa ba ne. Ni dai na yi imani shugaban ƙasa ya kamata na fara nunawa kafin na zo nan.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: INEC ta mika takardar shaidar lashe zabe ga Aiyedatiwa

"To amma tun da ina Abuja shiyasa na zo, na san aikin da Ganduje ya yi wa APC a matakin ƙasa da jiha, tun da ya karbi shugabancin jam'iyya ba nu faɗi zaɓe ba."

- Lucky Aiyedatiwa.

Ganduje ya yi murna da nasarar Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da nasarorin da suke samu a zaɓukan gwamnoni.

Ganduje ya bayyana cewa nasarar da APC ke samu alama ce da ke nuna za ta daɗe kan madafun iko domin ta samu karɓuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262