"Dan Allah Ka Hakura," Jigon PDP Ya Ba Atiku Shawara kan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Jigon PDP, Bode George ya bukaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya hakura da takara a zaben 2023
- George, tsohon mataimakin shugaban PDP ya ce lokaci ya yi da Atiku zai koma gefe bayan shekaru 31 yana neman mulkin Najeriya
- Ya ce Atiku na cikin waɗanda suka taimakawa Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a zaɓen shugaban kasa na 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya bukaci Atiku Abubakar ya hakura da burinsa na zama shugaban kasa.
Geroge ya kuma shawarci tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya koma gefe, ka da ya nemi tsayawa takara a babban zaɓen 2027 mai zuwa.
2027: Jigon PDP ya buƙaci Atiku ya hakura
Jigon PDP ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a jihar Legas jiya Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tun 1993 Atiku ke neman zama shugaban ƙasa kuma har yau Allah bai ba shi nasara ba, dok haka lokaci ya yi da zai yi wa kansa karatun ta natsu.
Bode George ya ƙara da cewa jam'iyyar PDP ba ta mutum ɗaya ba ce don haka ya kamata Atiku ya matsa ya ba wasu dama su gwada sana'arsu.
"Atiku ya taimaki Tinubu a 2023" - George
A ruwayar Punch, Bode George ya ce
"A lokacin kakar zaɓen 2023, na fito na yi ta magana kan rikicin da ya ɓarke wanda ya samo daga burin Atiku, Iyorchia Ayu, David Mark da wasu.
"Yanzu ina Ayu? Ina ganin Atiku da Ayu ne suka share wa Bola Tinubu hanya ya zama shugaban ƙasa. Meyasa Atiku ya ƙagu ne? Ba za mu bari a rusa jam'iyyarmu ta PDP ba.
" Shawarar da zan ba Atiku ita ce a 2027 zai cika shekara 81 a duniya kuma tun 1993 yake neman kujrar shugaban ƙasa, lokaci ya yi da zaka hakura, ina rokonka dan Allah ka haƙura haka nan."
Atiku ya nuna damuwa da ciyo bashin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nuna bacin rai kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ciwo bashi.
Atiku Abubakar ya ce abin takaici ne a cigaba da ciwo bashi bayan Najeriya ta zamo kasa ta uku da ta fi tarin bashi a fadin duniya
Asali: Legit.ng