An Samu Rabuwar Kai a APC kan Zargin Sakataren Gwamnatin Tinubu da Ƙabilanci
- Kungiyar APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta kuma kokawa kan abin da ta ke gani kamar rashin adalci ne a gwamnatin Tinubu
- Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga ya ce su na zargin Sakataren gwamnati, George Akume da nuna wariya da ƙabilanci
- Sabon koken na zuwa ne bayan ƙungiyar Zazzaga ta ja daga a baya da zaman Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - Tsuguno ba ta ƙare a rikicin APC ba yayin da reshen jam'iyyar, shiyyar Arewa ta Tsakiya ke zargin gwamnati da nuna wariya.
An samu koken bayan an samu daidaito da ƙyar a kan kukan cewa Arewa ta Tsakiya ce ta dace ta jagoranci APC a matakin kasa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sabon korafin shiyyar na zargin Sakataren gwamnati, George Akume da nuna tsantsar ƙabilanci da wariya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zargin ƙabilanci a gwamnatin Tinubu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa kungiyar APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta ce masu ruwa da tsaki a yankin na kokawa da yadda Sakataren gwamnati ke ware su.
Wannan na a matsayin martani ga mai magana da yawun Akume, Terrence Kuanum na cewa zargin mai gidansa da ƙabilanci son ɓata masa suna ne kawai.
"Tiv Sakataren gwamnatin Tinubu ke so," Zazzaga
Shugaban kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ya zargi George Akume da nuna fifiko ga yan ƙabilar Tiv a shiyyar wajen naɗa muƙamai.
Saleh Zazzaga ya ce bakin masu ruwa da tsaki a shiyyar ya zo ɗaya, inda su ka fusata kan yadda Akume ke zaɓo mutane daga ƙabilarsa wajen samun muƙamai.
Gwamnatin Tinubu da yankin Arewa
A baya kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jinjina irin muhimmancin da cigaban Arewa ke da shi a wajen samun ƙasa mai yalwar arziƙi da kwanciyar hankali.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya bayyana haka, ya ƙara da cewa matuƙar Arewa ta samu matsala, lamarin zai shafi dukkanin sassan Najeriya.
Asali: Legit.ng