Taron NEC: Ciyamomin PDP na Jihohi 36 Sun Yanke Shawara kan Kujerar Damagum
- Umar Damagum ya kara samun goyon bayan ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam'iyyar PDP ta ƙasa
- Shugabannin PDP na jihohi 36 sun jaddada goyon bayansu ga Damagum a wani taro da suka yi a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja
- Wannan dai na zuwa ne a lokacin da PDP ke tunkarar taron majalisar zartawa watau NEC wanda aka tsara yi ranar 28 ga Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Muƙaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum ya jagoranci wani muhimmin taro da shugabannin jam’iyyar PDP na jihohi 36 a ranar Laraba a Abuja.
Wannan taro na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar PDP ke shirye-shiryen taron majalisar zataswa (NEC) ta kasa wanda za a yi ranar 28 ga watan Nuwamba.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa taron ya gudana ne a hedkwatar PDP da ke Wadata Plaza a Abuja ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ciyamomin PDP na goyon bayan Damagum
A wurin wannan taro, Damagum da ciyamomin PDP na jihohin Najeriya sun musanta raɗe-raɗen cewa shugaban jam'iyyar na fuskantar barazanar tsigewa.
Har ila yau, bayan taron ciyamomin jihohin sun jaddada goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP Umar Damagum.
A hira da aka yi da su, shugabannin sun bayyana babu wani abin damuwa ko barazana ga kujerar Damagum a taron NEC da ke tafe.
Damagum: Menene dalilin kiran taron?
A nasa jawabin, Damagum ya ce shugabannin PDP na jihohi sun kawo masa ziyara ne kamar yadda aka saba, saɓanin raɗe-raɗin da ake cewa ba su jituwa.
"Wannan taron ba sabo ba ne, dama mu kan haɗu mu tattauna a baya, ba yau ne karon farko ba, mun shirya wannan zama ne domin tattaunawa da ciyamomin jihohi.
"Idan kuka duba galibin shugabannin jam'iyya na jihohi ba a daɗe da zaɓensu ba, kusan duk sababbi ne, don haka mun kira wannan zama ne mu san juna amma ba shi da alaƙa da NEC."
Wani ɗan PDP a Katsina, Ahmad Sani Dogo, ya shaidawa Legit Hausa cewa da wahala a kawo ƙarshen taƙaddamar shugabancin jam'iyyar nan kusa.
A cewarsa, rikicin PDP ba wai a matakin kasa kaɗai ya tsaya ba, har a gundumomi da ƙananan hukumomi ana rigima kan shugabanci.
Ahmad ya ce matukar ba za a cire son rai, a hukunta duk wanda ya yi ba daidai ba tun daga sama har ƙasa to ba ranar karewar wannan rikicin.
"Idan ka duba daga an ɗinke nan can zai ɓalle, yanzu ciyamomi sun ce sun tare da Damagum, shi kuma alamu sun nuna yana tare da Wike, wanda har yanzun an gaza hukunta shi.
"Ina dokokin jam'iyya suke, meyasa ba za a ajiye son rai a koma kan tushe ba, ni ina ganin idan har a haka za a tafi, to babu ranar da wannan matsalar za ta kau," in ji shi.
PDP ta yi watsi da sakamkon zaben Ondo
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Ondo ta bayyana cewa ba ta gamsu da sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar a jihar ba.
PDP ta bayyana cewa za ta garzaya kotu domin ƙalubalantar nasarar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya samu a zaɓen na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng