'Tinubu Bai San Ya Aka Yi ba': Ganduje Ya Fadi Yadda Suka Yi Nasara a Zaben Ondo

'Tinubu Bai San Ya Aka Yi ba': Ganduje Ya Fadi Yadda Suka Yi Nasara a Zaben Ondo

  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kokarin da suka yi wurin tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a jihar
  • Ganduje ya ce al'ummar jihar Ondo masu son cigaba ne shiyasa suka zabi Gwamna Lucky Aiyedatiwa a makon da ya gabata
  • Wannan na zuwa yayin da shugaban APC ya karbi bakuncin Aiyedatiwa da kuma mataimakinsa a yau a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya sake yin magana kan zaben jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.

Ganduje ya tabbatar da cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara ba tare da saka baki daga fadar shugaban kasa ba.

Ganduje ya sake magana kan zaben jihar Ondo
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce sun yi nasara a zaben Ondo ba tare da sanya hannun Bola Tinubu ba. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Ganduje ya sake bugan kirji bayan zaɓen Ondo

Kara karanta wannan

Zaɓen Ondo: Jerin manyan waɗanda suka yi nasara da waɗanda tafka asara

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana haka ne a yau Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024 a sakatariyar jam'iyyar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya kuma ce nasarar APC a Ondo ya kara tabbatar da rugujewar jam'iyyar PDP mai adawa, Vanguard ta tabbatar.

"Wannan wani lamari ne da ya samu karɓuwa daga mutane, al'umma sun nuna maka goyon baya."
"Dole mu taya ka murna kan wannan gagarumar masara da ka samu, na san yan Ondo suna son cigaba shiyasa suka goya maka baya."

- Abdullahi Ganduje

Gwamna Aiyedatiwa ya yi godiya ga APC

A martaninsa, Gwamna Aiyedatiwa ya godewa shugabannin jam'iyyar APC kan irin goyon baya da suka ba shi har ya kai ga samun nasara.

Aiyedatiwa ya kuma godewa al'ummar jihar Ondo inda ya ba su tabbacin cigaba da wadatar da su da ayyukan more rayuwa.

Ganduje ya magantu kan zaben Ondo

Kara karanta wannan

Hadin kan APC ya na tangal tangal, gwamna ya gargadi masu son rikita jam'iyya

Kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben Ondo.

Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan irin gudunmawa da goyon baya da yake ba jam'iyyar APC wanda yake taimakonta a zabuka.

Wannan na zuwa ne bayan hukumar zabe ta INEC ta sanar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.