Ondo 2024: Muhamman Dalilai 5 da Suka Sa PDP Ta Sha Kashi a Zaben Gwamna

Ondo 2024: Muhamman Dalilai 5 da Suka Sa PDP Ta Sha Kashi a Zaben Gwamna

Ondo - A ranar Asabar da ta gabata, 16 ga watan Nuwamba, 2024, aka gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayan kammala tattara sakamako, hukumar zaɓe INEC ta sanar da Gwamna Lucky Auyedatiwa na APC a matsayin wanda ya samu nasara da gagarumin rinjaye.

Gwamna Aiyedatiwa da Ajayi.
Abubuwan da suka taka rawa wajen kayar da PDP a zaben Ondo Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa, Agboola Ajayi
Asali: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa Aiyedatiwa ya samu kuri’u 366,781 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Agboola Ajayi na PDP, wanda ya samu kuri’u 117,845.

Wannan dai shi ne mafi munin rashin nasara da jam'iyyar PDP ta yi a zaɓen gwamnan jihar Ondo tun 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zabukan gwamnoni shida da aka yi a Ondo, PDP ta samu kuri’u 195,682 (1999), 655,968 (2003), 349,258 (2007), 155,961 (2012), 150,380 (2016), da 195,791 (2020).

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna ya tashi da kuri'u 1,162, ya fadi wanda ya jawo ya fadi zaben Ondo

Zaben gwamnan kuma shi ne mafi muni ta fuskar fitowar masu kada kuri’a, lamarin da ke nuna yadda mutane suka fara cire rai da zaɓe a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ce a zaɓen da aka yi ranar Asabar, kudi sun taka rawa matuƙa saboda yadda jam'iyyu suka rika sayen kuri'u tsakanin N5,000 zuwa N20,000.

Abubuwan da suka kayar da PDP a Ondo

Aiyedatiwa ya yi nasara da gagarumin rinjaye a dukkan mazaɓun sanatoci uku a jihar wanda ke nuna yadda ya samu karɓuwa a jihar Ondo.

Haka nan ɗan takarar PDP, Ajayi ya kasa kawo karamar hukumarsa ta Ese-Odo, inda ya samu kuri’u 7,814 yayin da Gwamna Aiyedatiwa ya samu kuri’u 14,511.

Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da ake ganin sune suka jawo wa PDP wannan rashin nasara mafi muni tun 1999.

1. Tasirin Shugaba Tinubu a jihar Ondo

Wasu majiyoyi sun nuna cewa tun kafin zaɓen, shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gana da manyan APC a jihar Ondo kuma ya umarci su tabbatar da jam'iyyar ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Yadda APC ta sha ruwan kuri'u, Aiyedatiwa ya koma kujerar gwamnan Ondo

Zaben Ondo dai shi ne na farko da aka gudanar a shiyyar Kudu maso Yamma tun bayan rantsar da shugaba Bola Tinubu, wanda ya fito daga yankin.

Wannan dalilin ya sa jagororin APC suka ja hankalin Gwamna Aiyedatiwa da sauran shugabannin jam'iyya cewa bai kamata Tinubu ya ji kunya a shiyyarsa ba.

2. Zuwan gwamnonin APC Ondo

Akalla gwamnonin APC tara ne suka je Ondo tare da shugabannin jam'iyyar karashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya wallafa hotunan lokacin da suke sa ido kan yadda ake tattara sakamako a shafinsa na Facebook.

An ruwaito cewa Aiyedatiwa ya gana da wasu gwamnonin kuma ya roke su da kada su bar shi ya tunkari zaben shi kaɗai.

Ana ganin dai gwamnonin APC sun ba da gudummuwa matuka wajen kayar da PDP a zaben da aka kammala a Ondo.

3. Rikicin cikin gida a PDP

Kara karanta wannan

An kammala zaben Ondo, INEC ta fadi wanda ya yi nasara, an jero kuri'un APC, PDP

Saɓanin Aiyedatiwa wanda ya samu nasarar shawo kan sauran ƴan takarar APC bayan zaɓen fidda gwani, ɗan takarar PDP Ajayi ya gaza haɗa kan ƴan jam'iyyar

Rikicin da ya biyo bayan zaben fidda ɗan takarar PDP a jihar Ondo ya fusata manyan kusoshi da jiga-jigan jam'iyya, da yawansu suka sauya sheƙa.

Ƴan takarar gwamna biyu suka bar PDP kafin zaɓe, Olusola Ebiseni ya koma LP yayin da Bamidele Akingboye ya koma SDP kuma aka tsayar da shi takara.

4. Rashin goyon bayan Mimiko

Tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko, wanda ya kasance babban abokin Ajayi, ya tsaya a tsakiya a lokacin kamfe, ya ƙi nuna cikakken goyon bayan PDP.

Ana ganin da Mimiko ya marawa ɗan takarar PDP baya, da jam'iyyar APC da Aiyedatiwa sun sha wahala ko da kuwa za su lashe zaɓen.

5. Tasirin jam'iyya mai mulki

A matsayin gwamna mai ci, Lucky Aiyedatiwa yana da karfin mulki a hannunsa wanda ya ba shi wata dama fiye da sauran ƴan tsagin adawa.

Kara karanta wannan

Ogun: Jam'iyyun adawa na so a sake zabe yayin da APC ta lashe kujerun ciyamomi 20

Ma'aikatan gwamnati, sarakuna, manoma da sauran masu ruwa da tsaki sun mara masa baya tun kafin ranar zaɓe.

Watanni ƙalilan gabanin zaben, Aiyedatiwa ya nada mataimaka 344 tare da umartarsu da su koma mazabunsu domin yada nasarorin da ya samu.

'APC za ta daɗe tana mulki' - Ganduje

A wani rahoto, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da nasarorin da suke samu a zaɓukan gwamnoni.

Ganduje ya bayyana cewa nasarar da APC ke samu alama ce da ke nuna za ta daɗe kan madafun iko domin ta samu karɓuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262