Gwamna Ya Samu Karin Dama daga Majalisa, Zai Naɗa Sababbin Hadimai 20

Gwamna Ya Samu Karin Dama daga Majalisa, Zai Naɗa Sababbin Hadimai 20

  • Majalisar dokokin jihar Edo ta amince Gwamna Monday Okpebholo ya naɗa masu ba shi shawara ta musamman har guda 20
  • Gwamnan ya buƙaci naɗa hadimai 20 ne domin taimaka masa wajen gudanar da harkokin gwamnatin jihar da ke Kudu maso Kudu
  • Har ila yau, Gwamna Okpebholo ya miƙa sunan sabon kwamiahinan kudi da ya naɗa ga majalisar dokokin domin tantancewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Majalisar dokokin jihar Taraba ta amince da bukatar Gwamna Monday Okpebholo ta naɗa sababbin hadimai 20 da za su taimaka masa.

Gwamna, wanda ya karɓi rantsuwar kama aiki a makon jiya, ya buƙaci majalisar ta sahale masa ya naɗa hadiman da za su kama masa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Gwamna Okpebholo na jihar Edo.
Majalisar dokokin Edo ta amince da bukatar Gwamna Okpebholo ta nada hadimai 20 Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

The Nation ta tattaro cewa ƴan majalisa 24 sun amince da bukatar mai girma gwamna a zamansu na yau Talata, 19 ga watan Nowamba, 2023.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince Bola Tinubu ya karɓo bashin Naira tiriliyan 1.77

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Edo ya samu dama daga majalisa

Tun farko dai sakataren gwamnatin Edo, (SSG), Musa Ikhilor ya miƙawa majalisar takardar neman amincewarta kan naɗa hadiman Gwamna Okoebholo.

Bayan karanta sakon, shugaban masu rinjaye, Charity Aiguobarueghian ya mike ya gabatar da kudirin amincewa da bukatar kamar yadda doka ta tanada.

Aiguobarueghian ya kafa hujja da sashe na 196 (2) na kundin tsarin mulki na 1999, wanda ya bai wa gwamna ikon nada masu ba da shawara na musamman.

Majalisar Edo ta amince da bukatar gwamna

Nan take dai kudirin ya samu goyon bayan dukkan ƴan majalisar dokokin yayin da aka kaɗa kuri'ar murya.

Hakan ya sa kakakin majalisar dokokin, Hon.Blessing Agbebaku ya amincewa gwamnan ya naɗa masu ba shi shawara ta musamman har guda 20.

Bugu da kari, majalisar ta kuma samu wasiƙa daga Gwamna Okpebholo, inda ya nemi ta amince da wanda ya naɗa a matsayin kwamishinan kudi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi zazzaga, ya mallami ma'aikata a manyan makarantu da asibitoci

Gwamnan Edo ya rufe asusun gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya rushe wata ma'aikata da gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira.

Gwamna Okpebholo ya kuma umarci rufe asusun jihar da ke dukan bankunan yan kasuwa har sai an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262