Hadin Kan APC Ya na Tangal Tangal, Gwamna Ya Gargadi Masu Son Rikita Jam'iyya
- Gwamnan jihar Jigawa, Umar A. Namadi ya dawo gida bayan shafe kwanaki 18 a kasar waje inda ya tarar da wani rikici a cikin jam'iyyar APC
- Mai girma Namadi ya gargadi masu neman raba jam'iyyar gida biyu inda ya tabbatar da cewa APC za ta cigaba da zama daya a jihar Jigawa
- Al'ummar jihar Jigawa sun yi dandazo domin tarbar gwamnan yayin da ya shiga birnin Dutse bayan sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa ya dawo gida bayan hutun kwanaki 18 da ya dauka zuwa kasashen waje.
Yayin da ya dawo jihar Jigawa, gwamna Namadi ya samu wani rikici da ya ɓulla a jam'iyyar APC kan shugabanci.
Hadimin gwamna Namadi, Garba Muhammad ya wallafa yadda aka tarbi gwamnan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Jigawa ya gargadi masu son raba APC
Gwamna Umar A. Namadi ya bayyana cewa a lokacin da ya tafi kasar waje ya samu labarin wani yunkurin raba APC gida biyu a Jigawa.
A karkashin haka, gwamnan ya ce duk yadda za a yi, APC za ta cigaba da zama jam'iyya daya a Jigawa.
Umar Namadi ya ce dole ne mutane su rika hakuri a tsakaninsu saboda samun nasara mai dorewa a jihar.
"A lokacin da na tafi, na ji labarin wasu abubuwa da suka faru da ban ji dadinsu ba. Alal misali, muna da bangare daya ne na APC a Jigawa.
Dole mu mayar da hankali waje daya. Ba za mu yarda a kawo wani abu da zai raba mana hankali ba.
Akwai wadanda idan suka ga ana cigaba ta hanyar da ba su so, za su yi kokarin kawo rabuwar kai. Bai kamata mu bar irin mutanen nan su yi nasara ba."
- Umar Namadi
Gwamna Umar Namadi ya yi godiya ga al'ummar jihar Jigawa bisa kyakkyawar tarba da suka masa bayan dawowarsa.
APC ta rabu 2 a jihar Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Sakoto, Ahmed Aliyu zai iya fuskantar matsala bayan wasu daga cikin yan jam'iyyarsa ta APC sun daina goyon bayansa.
APC ta rabu, yayin da wasu daga cikin yan jam'iyyar su ka ware kansu karkashin jagorancin Ibrahim Lamido domin kalubalantar gwamnan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng