Ganduje Ya Sake Kada Hantar 'Yan Adawa bayan Nasarar APC a Ondo

Ganduje Ya Sake Kada Hantar 'Yan Adawa bayan Nasarar APC a Ondo

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da nasarorin da suke samu a zaɓukan gwamnoni
  • Ganduje ya bayyana cewa nasarar da APC ke samu alama ce da ke nuna za ta daɗe kan madafun iko domin ta samu karɓuwa
  • Shugaban na APC ya yabawa hukumar zaɓe ta INEC kan yadda ta gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan nasarorin da jam'iyyar ke ci gaba da samu a Najeriya.

Ganduje ya yi hasashen cewa yadda jam’iyyar APC ke ƙara samun karɓuwa a ƙasar nan alama ce da ke nuna za ta daɗe tana mulki.

Ganduje ya yi magana kan nasarar APC
Ganduje ya ce APC za ta dade kan madafun iko Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Abdullahi Ganduje ya yi hasashen mulkin APC

Kalaman na Ganduje na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

'Mun gode Tinubu': Ganduje ya taya Aiyedatiwa murna, ya fadi jihohi 2 da za su kwace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya yi kalaman ne yayin da yake mayar da martani kan sake zaɓen Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da aka yi.

"Nasarorin da jam'iyyarmu ta samu a jihohin Edo da Ondo ba abin wasa ba ne, alama ce da ke nuna ƴan Najeriya sun rungumi APC a matsayin jam'iyyarsu tare da tabbacin cewa za ta daɗe kan madafun iko."
"Nasarar Ayedatiwa ba nasara ce ga APC kawai ba, amma nasara ce ga dimokuradiyya da kuma cikar muradun jama'a."

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya yabawa hukumar INEC

Shugaban jam’iyyar APC ya yabawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) bisa gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana, wanda ke ƙara ƙarfafa ribar dimokradiyyar Najeriya, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ganduje ya kuma yabawa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan yadda suka tabbatar da samar da yanayi mai kyau ga masu kaɗa ƙuri’a domin gudanar da zaɓensu cikin walwala.

Kara karanta wannan

Ondo: INEC ta sanar da sakamakon rumfar zaben Gwamna Aiyedatiwa na APC

APC ta lashe zaɓen gwamnan Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da sakamakon zaben jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.

Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng