'Mun Gode Tinubu': Ganduje Ya Taya Aiyedatiwa Murna, Ya Fadi Jihohi 2 da Za Su Kwace

'Mun Gode Tinubu': Ganduje Ya Taya Aiyedatiwa Murna, Ya Fadi Jihohi 2 da Za Su Kwace

  • Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben Ondo
  • Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan irin gudunmawa da goyon baya da yake ba jam'iyyar APC
  • Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanar da Aiyedatiwa na APC wanda ya lashe zaben da aka gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya yi magana bayan nasararsu a zaben jihar Ondo da aka yi.

Ganduje ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC murnar lashe zaben Ondo.

Ganduje ya yi magana kan zaben gwamnan Ondo
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya fadi jihohin da za su kwace bayan nasara a Ondo. Hoto: All Progressives Congress, Hon. Lucky Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

Ganduje ya sha alwashin kwace jihohi 2

Tsohon gwamnan Kano ya fadi haka ne jim kaɗan bayan hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben, cewar DCL Hausa.

Kara karanta wannan

An kammala zaben Ondo, INEC ta fadi wanda ya yi nasara, an jero kuri'un APC, PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya bayyana jihohin Oyo da Osun a matsayin wadanda za su sakawa kahon-zuka domin kwace su.

Daga bisani, Ganduje ya yi godiya ga Shugaba Bola Tinubu kan irin goyon bayan da yake ba jam'iyyar, cewar rahoton TheCable.

Ganduje ya yabawa Tinubu kan kokarinsa

Ganduje ya ce gudunmawar Tinubu na da alaƙa da nasarar da jam'iyyar APC ke samu a zabukan da ake gudanarwa.

"Abin da muka sanya a gaba shi ne wannan yanki na Kudu maso Yamma, kun san mun kware a samun abin da muke nema."
"Za mu yi duk mai yiwuwa domin ganin mun hada su a cikin jihohin da muke rike da su a hannunmu."

- Abdullahi Ganduje

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar Osun a shekarar 2016 mai zuwa.

Aiyedatiwa ya lashe zaben gwamnan Ondo

Kun ji cewa Hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Ondo: Dan takarar PDP ya ga ta kansa, ya fadi kulle kullen da APC ta shirya

Farfesa Olayemi Akinwunmi, baturen zabe a jihar shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Gwamna Aiyedatiwa na APC ya samu kuri'u 366,781 yayin dan takarar PDP, Ajayi Agboola ya samu kuri'u 117,845 a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.