An Kammala Zaben Ondo, INEC Ta Fadi Wanda Ya Yi Nasara, An Jero Kuri'un APC, PDP
- Hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Ondo
- Farfesa Olayemi Akinwunmi, baturen zabe a jihar shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki
- Gwamna Aiyedatiwa na APC ya samu kuri'u 366,781 yayin dan takarar PDP, Ajayi Agboola ya samu kuri'u 117,845 a zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Hukumar INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
APC ta lashe kananan hukumomi 18 a Ondo
TheCable ta ruwaito cewa INEC ta kammala tattara sakamakon zaben da aka yi a kananan hukumomi 18 da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baturen zabe a jihar, Farfesa Olayemi Akinwunmi shi ya sanar da sakamakon zaben a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024 a birnin Akure.
An fafata tsakanin jam'iyyu da dama inda APC ta yi nasara yayin da PDP ke biye mata a matsayi na biyu.
Jam'iyyar ZLP ta ba da mamaki a Ondo
Jam'iyyar ZLP ita ta kasance ta uku a zaben da aka gudanar wanda wasu mazauna Ondo suka ce ba a samu tashin hankali ba a zaben.
Gwamna Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 366,781 yayin da PDP mai adawa ta damu kuri'u 117,845, cewar Channels TV.
Jam'iyya mai adawa ta ZLP ta samu kuri'u 2,692 yayin da jam'iyyar LP ta bangaren Peter Obi ta tashi da kuri'u 1,162.
PDP ta zargi badakala a zaben Ondo
Tun farko, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta fara korafi kan zaben da ake cigaba da tattarawa a jihar Ondo inda ta zargi hukumar INEC da rashin shiri.
Dan takarar PDP, Ajayi Agboola ya nuna damuwa kan yadda aka yi ta samun korafe-korafe a zaben da aka gudanar a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ke kan gaba a zaben inda ya lashe kananan hukumomi 15 daga 18.
Asali: Legit.ng