Sakamakon Zaben Ondo: Jerin Kananan Hukumomi 15 da Jam'iyyar APC Ta Lashe
- Jam'iyyar APC ta yiwa babbar abokiyar hamayyarta, watau PDP dakan sakwara a zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 15 yayin da ake jiran isowar sauran uku
- Sai dai daga iya kananan hukumomi 15 da aka bayyana, APC ta lashe dukkaninsu ba tare da PDP ta samu nasara ko a guda daya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo daga aka gudanar 17 ga Nuwamba.
A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwambar nan ne aka gudanar da zaben gwamnan jihar yayin da INEC ta kuduri aniyar ayyana wanda ya alashe zabena a ranar Lahadi.
Sakamakon zaben gwamnan Ondo
Jaridar The Punch ta rahoto cewa INEC ta rigaya ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 15 zuwa yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya rage saura sakamakon kananna hukumomi uku a kammala tattara sakamakon, INEC ta ce ta dage zaman zuwa karfe 12 na rana, inji rahoton Daily Trust.
A iya kananan hukumomi 15, INEC ta bayyana cewa jam'iyyar APC ta samu kuri'u 268,144 yayin da PDP ta samu kuri'u 79,125.
Jam'iyyar ZLP kuwa ta samu kuri'u 2312 yayin da LP ta samu kuri'u 404.
Kananan hukumomin da APC ta lashe
1. Okitipupa
APC - 26,811
PDP - 10,233
2. Akure ta Arewa
APC - 14,451
PDP - 5787
3. Akoko ta Kudu maso Gabas
APC - 12,140
PDP - 2,692
4. Owo
APC - 31, 914
PDP - 4,740
5. Akoko ta Kudu maso Yamma
APC - 29,700
PDP - 5,517
6. Ondo ta Yamma
APC - 20,755
PDP - 6,387
7. Ose
APC - 16,555
PDP - 4,472
8. Akoko ta Arewa maso Yamma
APC - 25,010
PDP - 5,502
9. Akure ta Kudu
APC - 32,969
PDP - 17,926
10. Akoko ta Arewa maso Gabas
APC - 25,657
PDP - 5,072
11. Ondo ta Gabas
APC - 8,163
PDP - 2,842
12. Irele
APC - 17,117
PDP - 6,601
13. Ele Oluji/Okeigbo
APC - 16,600
PDP - 4,442
14. Ifedore
APC - 14,157
PDP - 5,897
15. Idanre
APC - 9,114
PDP - 8,940
Asali: Legit.ng