Ondo 2024: INEC Ta Ɗage Tattara Sakamakon Zaben Gwamna, Ta Sanya Sabon Lokaci
Ondo - A safiyar Lahadi, 17 ga Nuwamba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da dage tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta sanar da cewa za ta dawo ci gaba da tattara sakamakon zaben ne da karfe 12 na ranar Lahadin.
Premium Times ta ruwaito cewa jami’in tattara sakamakon, Farfesa Olayemi Akinwunmi, ya bayyana hakan a Akure, babban birnin jihar Ondo.
INEC ta dage tattara sakamakon zabe
A cewar Akinwunmi, hukumar na da kwarin gwiwar cewa za ta iya kammala tattara dukkanin sakamakon zuwa yammacin ranar Lahadi.
Farfesa Akinwunmi ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina ganin za mu iya dage zaman zuwa karfe 12 na rana, jami'an kananan hukumomi biyu da suka rage ba su karaso ba, don haka mun dage zaman har zuwa karfe 12 na rana.
Kananan hukumomin, Ilaje da Ese Odo suna da nisa sosai, don haka muna bukatar mu jira lokacin isowarsu, amma za mu dawo karfe 12 na rana.”
An samu jinkirin tattara sakamako
Legit.ng ta fahimci cewa, an samu jinkirin tattara sakamakon kananan hukumomin da suka rage ne saboda matsalar zirga-zirga a wasu sassan jihar.
Ilaje, Ese Odo, da Odigbo sune kananan hukumomin da suka rage a bayyana sakamakon zabensu a hukumance.
Ya zuwa yanzu gwamnan jihar Ondo kuma dan takarar jam’iyyar APC, Lucky Ayedatiwa ne ke kan gaba a kananan hukumomi 15 yayin da INEC ta ke bayyana sakamakon zaben.
Babban abokin hamayyarsa shine Agboola Ajayi na jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng