Ondo: INEC Ta Sanar da Sakamakon Rumfar Zaben Gwamna Aiyedatiwa na APC
- Gwamna Lucky Aiyeɗatiwa na jam'iyyar APC ya samu nasarar doke manyan abokan hamayyarsa a sakamakon zaben rumfarsa a Ondo
- Jami'an INEC sun sanar da cewa APC ta samu ƙuri'u 128 yayin da PDP ta samu ƙuri'u 3 a rumfar da gwamnan ya kaɗa kuri'arsa yau Asabar
- Tun farko dai gwamnan ya ce matukar zaben ya karkare cikin lumana, yana da ƙwarin guiwar samun nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe sakamakon zabe a rumfar da ya ƙaɗa kuri'a a jihar Ondo.
Gwamna Aiyedatiwa, wanda ke fafutukar ci gaba da mulki, ya kaɗa kuri'a ne a rumfar zaɓe mai lamba 5, Ugbo Ward 4, Obenla da ke karamar hukumar Ilaje.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa bayan kammala kaɗa ƙuri'a da ƙidayawa a rumfar zaben, Aiyedatiwa, ɗan takarar a inuwar APC ya doke abokan hamayyarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon mazaɓar Gwamna Aiyedatiwa
Lucky Aiyedatiwa ya samu kuri'u 128, inda ya doke babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP, Agboola Ajayi wanda ya samu ƙuri'u uku kadai.
Tun farko dai Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana ƙwarin guiwar cewa duba da yadda zaben ke tafiya cikin lumana, shi zai samu nasara a ƙarshe.
Gwamnan ya ce:
"Ina da yaƙinin za a kammala zaɓen nan lami lafiya kuma za a yi sahihin zaɓe, a bayanan da na samu kayan zaɓe sun isa rumfuna a kan lokaci, ya kamata mutane su fita su yi zaɓe."
Karanta wasu labaru game da zaben Ondo:
- Ondo 2024: Yadda ake cakewa mutane kuɗin Kuri'u a kusa da jami'an EFCC
- Dan takarar mataimakin gwamna na APC ya lallasa PDP a rumfar zabensa
- Ondo: 'Abin da zai saka ni karbar kaddara idan na fadi zabe': Dan takarar APC
Ondo: PDP ta zargi APC da sayen kuri'u
A wani labarin, an ji cewa jam'iyyar PDP ta zargi wasu jami'an APC da raba kudi ga al'umma da wasu kayayyaki domin jan hankulan mutane masu kada kuri'a.
Yayin da kada kuri'a ta fara nisa, hankula sun fara komawa kan yan takarar PDP da APC domin ganin yadda za su ƙare a zaben.
Asali: Legit.ng