Halin da Ake Ciki a Zamfara kan Zaben Kananan Hukumomi, an Samu Bayanai

Halin da Ake Ciki a Zamfara kan Zaben Kananan Hukumomi, an Samu Bayanai

  • Zaben kananan hukumomi a jihar Zamfara ya ci karo da matsala saboda rashin fitowa da al'umma suka yi
  • Hukumar zaben jihar (ZASIEC) ta shirya zaben ne a kananan hukumomi 14 da na kansiloli a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024
  • Sai dai al'umma da dama sun ki fitowa zaben inda suka cigaba da lamuransu na yau da kullum musamman a birnin Gusau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - An gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Zamfara a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.

Sai dai al'umma da dama ba su fito zaben ba kamar yadda ake tsammani yayin da suke cigaba da gudanar lamuransu.

Wasu yan Zamfara sun kauracewa zaben kananan hukumomi
An gudanar da zaben kananan hukumomi a Zamfara, mutane da yawa sun kaucewa zaɓen. Hoto: Dauda Lawal.
Asali: Twitter

Zamfara: An gudanar da zaben kananan hukumomi

Channels TV ta ce wasu yan birnin Gusau da dama sun bubbude shagunansu yayin da ake gudanar da zaben.

Kara karanta wannan

Ondo: An tarwatsa masu zabe da miyagu suka yi ta harbe harbe, an gano dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar zaben jihar (ZASIEC) ita ta shirya zaben a kananan hukumomi 14 da na kansiloli da ke fadin jihar.

Sai dai mutane ba su fito zaben ba saboda wasu dalilansu na karan kansu wanda ya kashe armashin zaben da aka yi a yau Asabar.

Wasu sun fadi musabbabin rashin fitowa zabe

Wasu sun alakanta samun matsala a fitowar al'umma da cewa rashin wayar da kan mutane da hukumar zaben jihar ta yi.

Wani mai suna Abubakar Abubakar ya ce kwata-kwata bai san ma da zaben ba saboda haka dole ya bude shagonsa domin gudanar da kasuwanci.

Duk da rashin fitowa zaben, hukumar ta gudanar da zaben ba tare da samun matsala musamman a bangaren tsaro ba.

APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Nasarawa

Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa, ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 13 da ke faɗin jihar da aka gudanar.

Kara karanta wannan

'Abin da zai faru idan na fadi zaben gwamnan Ondo,' dan takarar SDP ya magantu

Shugaban hukumar NASIEC, Barista Ayuba Wandai ya bayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 13.

Hakazalika, Barista Wandai ya ce APC ta lashe mafi rinjayen kujerun kansilolin jihar a zaben da ya ce an gudanar cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.