Zaben Ondo: Dan Takarar Mataimakin Gwamna na APC Ya Lallasa PDP a Rumfar Zabensa

Zaben Ondo: Dan Takarar Mataimakin Gwamna na APC Ya Lallasa PDP a Rumfar Zabensa

  • Ɗan takarar mataimakin gwamna na APC a zaɓen gwamnan Ondo ya samu nasarar lashe zaɓe a rumfar zaɓensa
  • Jam'iyyar APC ta samu nasara a rumfar zaɓen da Olayide Adelami ya kaɗa ƙuri'a inda ta lallasa PDP mai adawa a jihar
  • Olayide Adelami ya nuna ƙwarin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaɓen gwamnan duba da irin karɓuwar da ta samu a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Ondo, Olayide Adelami, ya yi abin arziƙi a rumfar zaɓensa.

Olayide Adelami, ya samu nasarar lashe zaɓe a rumfar zaɓensa a zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.

APC ta yi nasara a rumfar zaben mataimakin gwamnan Ondo
Olayide Adelami ya lashe zabe a rumfar zabensa Hoto: Olayide Adelami, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jam'iyyar APC ta lashe zaɓen da ƙuri'u 209 a rumfar zaɓen da Olayide Adelami ya kaɗa ƙuri'arsa.

Kara karanta wannan

Ondo: INEC ta sanar da sakamakon rumfar zaben Gwamna Aiyedatiwa na APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta yi nasara a rumfar zaɓen Adelami

A rumfar zaɓe ta 16, Igboroko 2, gunduma ta 03, Ahmadiya Grammar School, Iselu, Owo, APC ta samu ƙuri’u 209, inda ta doke jam’iyyar PDP da ƙuri’u 11.

Olayide Adelami, wanda ya kaɗa ƙuri’arsa da misalin ƙarfe 9:40 na safe, ya yaba da yadda zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali, musamman a rumfar zaɓensa.

Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa ta APC za ta yi nasara, inda ya ba da misali da yadda suka yi yaƙin neman zaɓe da gaske da kuma karɓuwar da suka samu a faɗin ƙananan hukumomin jihar 18.

Rumfar zaɓen dai na da adadin masu kaɗa kuri’a 850 da suka yi rajista, wanda hakan ya nuna yadda jam’iyyar APC ta samu karɓuwa a wajen.

Rawar da Tinubu zai taka a zaɓen Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Zenith Labour Patry (ZLP) a Ondo, Dr. Abass Mimiko, ya yi magana kan rawar da Shugaba Bola Tinubu zai taka a zaɓen gwamnan jihar.

Abass Mimiko ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai tsoma baki a zaɓen gwamnan da ke gudana a jihar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng