Jigon APC Ya Faɗi Sirrin da Zai ba su Nasara a Zaben Ondo
- Yayin da ake cigaba da kada kuri'a, masana da yan siyasa na cigaba da bayyana ra'ayoyi kan wanda zai lashe zaben gwamnan jihar Ondo
- Wani jigo a APC, Olusola Oke ya ce ɗan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa ne zai lashe zaben cikin sauki saboda wasu dalilai na siyasa
- Olusola Oke ya nuna farin ciki kan yadda zaben ke tafiya cikin zaman lafiya tare da kira ga mutanen Ondo su kaucewa tarzoma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - A yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba hukumar INEC ke gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.
Wani kusa a APC, Olusola Oke ya ce ɗan takararsu, Lucky Aiyedatiwa ne zai lashe zaben da ake gudanarwa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Oke ya yi bayani ne bayan kada kuri'a a mazabarsa a wata hira da ya yi da yan jarida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oke: 'APC za ta lashe zaben Ondo'
Wani kusa a APC, Olusola Oke ya bugi kirji kan zaben da ake gudanarwa a jihar Ondo a yau Asabar.
Olusola Oke ya bayyana cewa dan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa zai kayar da yan jam'iyyun adawa cikin ruwan sanyi.
A cewar Oke, dama rana kawai suke jira su tabbatar da tara kuri'u ga Lucky Aiyedatiwa kuma lokaci ya yi.
"Babu wata jam'iyyar adawa mai karfi da za ta zamo barazana ga APC a jihar Ondo.
Ina mai tabbatar muku da cewa gwamna Lucky Aiyedatiwa zai lashe zabe cikin sauki kuma za mu tara masa kuri'u.
Mun dade muna jiran wannar rana. Alamu sun gama bayyana a kan Lucky Aiyedatiwa zai lashe zabe."
- Olusola Oke, jigon APC
Oke ya nuna farin ciki kan yadda zaben ke tafiya lafiya a sassan jihar da kuma yadda mutane suka fito kada kuri'a.
A karshe, dan siyasar ya buƙaci mutanen Ondo su kaucewa tarzoma domin tabbatar da an samu zaman lafiya har ƙarshen zaben.
PDP ta zargi APC a zaɓen Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta ce akwai yan APC da suke sayen kuri'u da karya dokokin zabe a jihar Ondo.
PDP ta yi kira ga hukumar EFCC da rundunar yan sandan Najeriya kan daukar mataki a kan yan APC da ta zarga da sayen kuri'u.
Asali: Legit.ng