Ondo: An Tarwatsa Masu Zabe da Miyagu Suka Yi Ta Harbe Harbe, an Gano Dalili
- An shiga fargaba bayan wasu miyagu sun yi ta harbe-harbe a kauyen Ofosun da ke jihar Ondo da safiyar yau Asabar
- Rahotannin sun tabbatar da cewa harbe-harben ya tilasta mazauna yankin shigewa gidajensu saboda fargaba
- Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kada kuri'a a zaben gwamna da ake yi a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Wasu miyagu sun rikita alummar yankin Ofosun da ke jihar Ondo ana cikin kada kuri'a a zaben da ake gudanarwa a yau Asabar.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 wanda ya tilasta mutane makalewa a gidajensu.
PDP ta zargi APC da kawo yan daba
Punch ta ce ba a tantance wadanda suka kai harin ba duk da dan takarar mataimakin gwamnan a jam'iyyar PDP ya zargi APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Festus Akingbaso ya nuna damuwa kan shigowar wasu yan daba a yankin da ke karamar hukumar Idanre.
Festus ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da daukar nauyin yan dabar zuwa kauyukan Ofosun da Omifunfun, cewar rahoton Vanguard.
Yada miyagu suka tarwatsa masu zabe a Ondo
Wani mazaunin yankin da ya bayyana kansa da Dauda ya yi magana kan harbe-harben inda ba su san wadanda ke da alhakin harbin ba.
"Ba mu san su waye ba ne amma sun yi ta harbe-harbe a sararin samaniyaa wasu yankunan Ofosun da ke Ondo kusa da iyakar jihar Edo."
- Cewar Dauda
PDP ta zargi APC da siyan kuri'u
Kun ji cewa mutanen jihar Ondo sun fara kada kuri'a a zaben gwamnan jihar da ke gudana a dukkan kananan hukumomi 18 a yau Asabar.
Jam'iyyar PDP ta zargi wasu jami'an APC da raba kudi ga al'umma da wasu kayayyaki domin jan hankulan mutane masu kada kuri'a.
Yayin da kada kuri'a ta fara nisa, hankula sun fara komawa kan yan takarar PDP da APC domin ganin yadda za su ƙare a zaben.
Asali: Legit.ng