Dan Takarar PDP Ya Gano babbar Matsala a Zaben Gwamnan Ondo, Ya Fara Sukar INEC

Dan Takarar PDP Ya Gano babbar Matsala a Zaben Gwamnan Ondo, Ya Fara Sukar INEC

  • Agboola Ajayi, dan takarar gwamnan Ondo a zaben jihar da ke gudana ya ce INEC ta gaza gudanar da sahihin zabe
  • Jim kadan bayan kada kuri'arsa, Agboola Ajayi ya yi ikirarin cewa na'urorin BVAS ba sa aiki yadda ya kamata a zaben jihar
  • Dan takarar ya kuma soki jami'an tsaro kan yin dafifi a rumfunan zabe, inda ya ce hakan na tsoratar da masu kada kuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Ondo, Agboola Ajayi, ya kada kuri’arsa a gundumar Apoi, mazaba ta 2, Kiribo, karamar hukumar Ese-Odo.

Agboola Ajayi ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da nuna son kai, yana cewa an samu jinkirin fara zabe a sassa da dama na jihar.

Kara karanta wannan

'Abin da zai faru idan na fadi zaben gwamnan Ondo,' dan takarar SDP ya magantu

Dan takarar PDP ya yi magana kan yadda zaben gwamnan Ondo ke gudana.
Agboola Ajayi: Dan takarar PDP ya caccaki INEC yayin da ake gudanar da zaben Ondo. Hoto: @A_AgboolaAjayi
Asali: Twitter

Dan takarar PDP ya soki INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta ce Ajayi ya bayyana takaici kan shafe kusan mintuna 10 kafin kada kuri’arsa, yana mai cewa irin wannan jinkirin zai tauye hakkin masu kada kuri’a.

Dan takarar na PDP ya kuma soki rashin ingancin na’urorin BVAS, yana cewa, “na’urorin ba sa aiki yadda ya kamata, wanda ya zama abin damuwa ga ingancin zaben."

Ya kuma yi tambihi kan yadda jami’an tsaro suke dafifi a kusa da rumfunan zabe, wanda ya ce hakan yana tsoratar da masu kada kuri’a.

PDP ta gano magudi a zaben Ondo

Dan takarar ya ce sun samu rahoton cewa an samu magudi, yana mai zargar INEC da kasa gudanar da sahihin zabe mai inganci a jihar, a cewar rahoton Tribune.

“An lalata tsarin,” a cewar dan takarar yayin da ya ke Allah wadai da gazawar INEC wajen gudanar da zabe mai inganci, duk da tarin alkawarin da ta yi.

Duk da wadannan kalubalen, Ajayi ya karfafa wa jama'a gwiwa akan su fita su kada kuri’a tare da kira ga hukumar INEC da ta gyara matsalolin don dawo da amana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.