Muhimman Abubuwa 6 kan Masu Kada Kuri'a a Zaben Ondo

Muhimman Abubuwa 6 kan Masu Kada Kuri'a a Zaben Ondo

  • A yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba aka fara kada kuri'a a zaben gwamna a jihar Ondo da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke yi
  • Jam'iyyun siyasa 17 ne suka shiga zaben domin karawa da dan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa da ke rike da madafun iko a jihar Ondo
  • A wannan rahoton, mun tatttaro muku wasu muhimman abubuwa da suka shafi masu kada kuri'a yayin da aka fara zaben gwamnan Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Mutane kusan miliyan 2 ne ake tsammanin za su ka da kuri'a a zaben gwamnan jihar Ondo.

A safiyar yau Asabar, 16 ga Nuwamba aka fara kada kuri'a a zaben kamar yadda hukumar INEC ta yi alkawarin hakan.

Zaben Ondo.
Muhimman abubuwa bayan kada kuri'a a zaben Ondo. Hoto: INEC
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta haɗa wani rahoto na musamman a kan adadin masu kada kuri'a da mazabun jihar.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ondo: Dalilan da za su iya sanya PDP ta lallasa APC a ranar Asabar

Abubuwa 6 kan masu zabe a jihar Ondo

1. Waɗanda suka yi rajista da INEC

Bincike ya tabbatar da cewa mutane 2,053,061 ne suka yi rajista da hukumar INEC domin mallakar katin kada kuri'a.

Sai dai ba dukkan mutanen ba ne suka samu damar karbar katinsu saboda wasu dalilai na daban.

2. Waɗanda suka karbi katin kada kuri'a

A cikin mutane 2,053,061 da suka yanki katin, mutum 1,757,205 ne suka karbi katin kada kuri'a daga hukumar INEC.

Saboda haka ake tsammanin mutane 1,757,205 din za su fito kada kuri'a yayin da aka fara zaben a yau.

3. Kananan hukumomin da za ayi zabe

A yanzu haka ana gudanar da zaben gwamna a Ondo ne a dukkan kananan hukumomin jihar su 18.

Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi alwashin cewa APC za ta lashe zabe a dukkan kananan hukumomin.

4. Unguwanni da za a yi zaben Ondo

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Dalilin da ya sa APC za ta iya lashe zaben gwamna na ranar Asabar

Rahotanni sun nuna cewa masu zabe za su kada kuri'a a zaben Ondo ne a unguwanni 203 a fadin jihar.

5. Wuraren kada kuri'a a unguwanni

A cikin unguwanni 203 na jihar, an tanadi wurare 3,933 da masu zabe za su kada kuri'a a fadin jihar Ondo

6. Adadin jam'iyyun siyasa a zaben Ondo

Jam'iyyun siyasa 17 ne za su fafata a zaben yayin da hankali ya fi karkata kan APC mai mulki a jihar da PDP.

Zaben Ondo: An kama mai sayen kuri'a

A wani rahoton, kun ji cewa wani bidiyo da ke yawo ya nuna lokacin da jami'an DSS suka cafke wani da ake zargin mai sayen kuri'u ne a zaben Ondo.

Rahoto ya nuna cewa an cafke mutumin ne a gunduma ta 4, rumfar zabe ta 007, da ke wajen makarantar St. Stephen, Akure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng