Zaben Ondo: Gwamna Ya Kaɗa Kuri'arsa, Ya Bayyana Irin Shagalin Murnar da Za Su Yi
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kaɗa kuri'a rumfar zabensa yayin da zaɓe ya kankama yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba a jihar Ondo
- Aiyedatiwa wanda ke takara a inuwar jam'iyyar APC ya nuna gansuwa da yadda zaben ke gudana, ya jinjinawa jami'an tsaro
- Da yake jawabi ga manema labarai, gwamnan ya bayyana kwarin guiwar samun nasara, inda ya ce za su yi bikin murna a APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamna Ƙucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya kaɗa kuri'arsa a zaben gwamnan da ke gudana yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba a jihar Ondo.
Gwamnan wanda ke takara a inuwar jam'iyyar APC ya jefa kuri'arsa a rumfar zaɓe mai lamba 5 da ke gunduma ta 5, Obenla a karamar hukumar Ilaje.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Gwaamna Aiyedatiwa ya kaɗa kuri'a bayan tantance shi da misalin karfe 8:52 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya gamsu da zaben Ondo
Da yake zantawa da manema labarai a wurin, Aiyedatiwa ya ce zaben na tafiya da kyau, sannan ya jinjinawa hukumar zaɓe INEC kan yadda take aikinta bisa tsari.
A rahoton Vanguard, gwamnan ya ce:
“Daga abin da na gani a nan yanzu haka, zabe na tafiya cikin lumana kuma na kada kuri’a ta. Ina jinjinawa hukumar INEC da jami'an tsaro bisa yadda suke aiki da nutsuwa.
"Saboda haka ina kira ga ɗaukacin mutanen Ondo su fito ƙwansu da kwarkwata su yi zaɓe ba tare da jin tsoron komai ba."
Gwamna ya ce APC za ta samu nasara
Lucky Aiyedatiwa ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa shi ne zai lashe wannan zaɓe da ake yi yau Asabar, yana mai cewa za su yi babban shagalin murna a APC.
Rahotanni sun nuna cewa an tura jami'an tsaron haɗin guiwa domin tabbatar da zaben ya tafi lami lafiya ba tare da wata tashin-tashina ba.
Ondo: Abin da zai iya ba PDP nasara
A wani rahoton, kun ji cewa akwai babbar dama ga jam’iyyar PDP na lashe zaben gwamnan jihar Ondo da za a yi a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba.
Agboola Ajayi, dan takarar PDP a zaben, yana da alaka mai karfi da ’yan jihar, wanda hakan na iya silar da zai samu rinjayen kuri'u.
Asali: Legit.ng