Ondo 2024: Dalilin da Ya Sa APC Za Ta Iya Lashe Zaben Gwamna Na Ranar Asabar
- Alamu sun nuna cewa jam’iyyar APC na da karfi sosai a zaben gwamnan Edo da za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba
- Baya ga kasancewarta jam’iyya mai mulki, gwamna jihar, Lucky Aiyedatiwa, yana da gogewar da zai iya sa APC ta samu nasara
- Har ila yau, APC ta kuduri aniyar lashe zaben kamar yadda ta yi a sauran zabukan baya-bayan nan a jihohin Edo, Imo da kuma Kogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya lashe zaben gwamnan jihar Ondo, wanda za a gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, saboda wasu dalilai.
Ana hasashen APC na iya lashe zaben saboda kasancewarta jam’iyya mai mulki a Ondo, duk da cewa ana ce-ce-ku-ce kan ayyukan da ta yi a jihar cikin shekaru 8 da suka gabata.
Rahoton Legit.ng ya nuna cewa jam’iyyar ta kuduri aniyar samun nasara, kamar yadda aka gani a zabukan gwamnoni da aka gudanar a jihohin Edo da Imo da kuma Kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene zai lashe zaben gwamnan Ondo?
Wannan kuduri da ta yi da kuma yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke gudanar da zaben, na iya baiwa jam’iyyar APC nasara a Ondo.
Bugu da kari, dan takarar jam’iyyar APC, Lucky Aiyedatiwa, ya yi fice, inda ya taba rike mukamin kwamishinan tarayya mai wakiltar jihar Ondo a hukumar raya Neja-Delta.
Hakazalika, Aiyedatiwa na kwarewar mulki kasancewar a kan kujerar gwamnan jihar tun bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar, Oluwarotimi Odunayo Akeredolu.
APC da PDP za su iya kai ruwa rana
Sai dai kuma abin lura a nan shi ne, ana sa ran za a iya kai ruwa rana tsakanin APC da PDP, inda dan takarar PDP, Agboola Ajayi, ke da nasa nasibin a siyar jihar Ondo.
A karshe dai sakamakon zaben zai dogara ne da abubuwa daban-daban da suka hada da fitowar masu kada kuri’a, dabarun yakin neman zabe, da kuma rawar da masu fada aji a jam’iyyar PDP ke takawa.
Haka kuma, Ajayi da Aiyedatiwa sun kasance tsofaffin mataimakan gwamnan jihar a karkashin marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu. Duka biyun sun dandana zakin mulkin jihar.
Wadanda za su iya lashe zaben Ondo
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna.
Zaben dai an ce zai kasance tamkar filin fafatawa tsakanin ‘yan takarar jam’iyyar APC, PDP, Labour Party da kuma SDP.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC da Agboola Ajayi na PDP duk sun kasance mataimakan gwamnoni ga marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu.
Asali: Legit.ng