Gwamna Ya Nada Sabon Kwamishina da Shugabannin Wasu Hukumomi 5 a Jiharsa

Gwamna Ya Nada Sabon Kwamishina da Shugabannin Wasu Hukumomi 5 a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya naɗa ƙarin kwamishina ɗaya da shugabannin wasu hukumomin gwamnati
  • Naɗe-naɗen na kunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Edo, Umar Ikhilor
  • Sanarwar ta ce waɗanda aka naɗa za su fara aiki ne daga ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo, ya amince da nadin wasu mutum shida a muƙamai daban-daban a gwamnatinsa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Umar Ikhilor ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba.

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo.
Gwamnan Edo ya naɗa kwamishinan kudi da shugabannin wasu hukumomin gwamnati Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da aka naɗa za su fara aiki ne daga jiya Juma'a, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya naɗa kwamishina da wasu 5

Kara karanta wannan

Zaɓen 2024: Muhimman abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da jihar Ondo

Waɗanda gwamnan ya nada sun hada da Dr. Emmanuel Iyamu a matsayin shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Edo.

Lucky Enehita-Inegbenehi a matsayin Manajan Darakta na hukumar kula da shara da CP Friday Ibadin (mai ritaya) a matsayin kwamandan hukumar tsaro ta jihar Edo.

Sai kuma Stainless Ijeghede a matsayin manajan darakta na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa da Lucky Eseigbe a matsayin manajan darakta na hukumar gine-gine.

Na ƙarshe shi ne Emmanuel Ehidiamen Okoebor wanda Gwamna Okpebholo ya naɗa a matsayin kwamishinan kudi idan majalisar dokoki ta amince da shi.

Gwamna Okpebholo ya naɗa masu gogewa

Sanarwar ta jaddada kudirin Gwamna Monday Okpebholo na zaƙulowa tare da naɗa kwararrun mutane waɗanda za su kawo ci gaba a jihar Edo.

Wani sashin sanarwar ya ce:

"Muna sanar da ɗaukacin al'umma cewa mai girma gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya amince da naɗin Dr. Iyamu a matsayin shugabam SUBEB."

Kara karanta wannan

Wutar Lantarki: Gwamna ya fusata, ya kori shugaban kamfanin IPCL nan take

Gwamna Okpebholo ya rufe asusun jihar Edo

A wani labarin, kun ji cewa kwanaki kaɗan da shiga ofis, Gwamna Monday Okpebholo ya rushe wata ma'aikata da gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira

Gwamna Okpebholo ya kuma umarci rufe asusun jihar da ke dukan bankunan yan kasuwa har sai an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262