Ondo 2024: Hukumar Zaɓe INEC Ta Canza Ɗan Takarar Gwamna Ana Gobe Zaɓe

Ondo 2024: Hukumar Zaɓe INEC Ta Canza Ɗan Takarar Gwamna Ana Gobe Zaɓe

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta maido da sunan Dr. Olorunfemi Ayodele Festus a matsayin ɗan takarar gwamnan LP a zaben gwamnan Ondo
  • INEC ta ɗauki wannan matakin ne bayan kotun ɗaukaka kara ta kori Olusola Ebiseni daga matsayin ɗan takarar LP tare da soke hukuncin FHC
  • Wannan sauyi na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa ɗa sa'o'i 24 a fara kaɗa kuri'a a zaben Ondo 2024 wanda aƙalla jam'iyyu 18 suke neman takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta maye gurbin dan takarar gwamnan Ondo a inuwar LP, Olusola Ebiseni da Dr. Olorunfemi Ayodele Festus.

INEC ta zare sunan Ebiseni tare da maye gurbinsa da Dr. Ayodele ne bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Muhimman abubuwa dangane da 'yan takara 4 a APC, PDP, SDP da LP

Farfesa Mahmud Yakubu.
Ondo: INEC ta maye gurbin Ebiseni da Festus a matsayin dan takarar gwamnan LP Hoto: INEC Nigeria
Asali: UGC

INEC ta maye gurbin ɗan takarar LP a Ondo

Hakan na kunshe ne a jerin sunayen ƴan takarar da za su fafata a zaben gwamnan Ondo da INEC ta wallafa a shafin X ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A gobe Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, al'ummar jihar Ondo za su fita rumfunan zaɓe su zaɓi wanda zai jagorance su na tsawon shekaru huɗu.

Hukumar INEC ta bayyana cewa ta canza ɗan takarar LP ne bayan samun takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ta asali (CTC).

Idan ba ku manta ba kotun ta kori Ebiseni daga matsayin ɗan takarar gwamna a inuwar LP, inda ta soke hukuncin babbar kotun tarayya.

Dalilin INEC na canza ɗan takarar LP

Sanarwar INEC ta ce:

"A watan Satumba, babbar kotun tarayya ta umarci INEC ta karɓi sunan Olusola Ebiseni a matsayin ɗan takarar gwamna a inuwa Labour Partya a zaben Ondo 2024.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo 2024: Cikakken jerin 'yan takarar gwamna a APC, PDP da sauran jam'iyyu

"Sai dai a ƙara mai lamba CA/ABJ/CV/1172/2024 da jam'iyyar LP ta ɗaukaka, kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin FHC bisa rashin cancanta."
"Domin biyayya ga umarnin kotu, INEC ta dawo da Olorunfemi Ayodele Festus a matsayin ɗan takarar LP a zaɓen gwamnan Ondo, 2024."

Sojoji sun tura dakaru zuwa jihar Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun tura jami'ansu zuwa Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamna na ranar Asabar.

'Yan sanda za su jagoranci tsaro na cikin gida, yayin da sojoji za su taimaka wajen ganin an gudanar da zaben cikin lumana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262