Hankalin PDP Ya Tashi, Ƴan Takarar Gwamnan Ondo 3 Sun Janye, Sun Marawa APC Baya
- 'Yan takara uku sun janye daga zaben gwamnan jihar Ondo, tare da goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC
- Dakta Ajibola Falaye, dan takarar jam'iyyar Accord, ya ce sun marawa Aiyedatiwa baya saboda jajircewarsa wajen kawo ci gaba
- Haka kuma, Hon. Jenyo Ataunoko na NRM da Olaide Rasheed Ibrahim na ADC, su ma sun nuna goyon baya ga Gwamnan Aiyedatiwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Kasa da sa’o’i 48 kafin zaben gwamna a jihar Ondo, ‘yan takara uku sun janye daga zabentare da marawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa baya.
Wadannan ‘yan takara sun fito ne daga jam’iyyun Accord Party, National Rescue Movement (NRM) da ADC, inda suka nuna gamsuwa da manufofin gwamnan.
Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo ce ta sanar da wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a yammacin Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan takara 3 sun goyi bayan Aiyedatiwa
'Yan takarar sun bayyana janyewarsu daga zaben a ziyarar goyon baya da suka kaiwa gwamnan, inda dan takarar Accord Party, ya yabawa manufofin Aiyedatiwa.
Dakta Ajibola Falaye, ya jinjina wa kokarin Aiyedatiwa wajen kawo ci gaba a jihar Ondo, tare da bayyana cewa ayyukansa sun sa jihar ta hau turba mai kyau.
Haka kuma, dan takarar NRM, Hon. Jenyo Ataunoko, da mataimakin dan takarar ADC, Mista Olaide Rasheed Ibrahim, su ma sun marawa gwamnan baya.
Aiyedatiwa na kara samun goyon baya
Wannan ci gaban ya kara karfafa takarar Aiyedatiwa, musamman ganin cewa dan takarar ADC ya rigaya ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan.
Dakta Falaye ya bayyana cewa shawarar marawa Aiyedatiwa baya ya samo asali ne daga jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima tun yana mataimakin gwamna.
Tare da wannan goyon baya daga wasu jam’iyyun, Gwamna Aiyedatiwa na kara samun karfi wajen ci gaba da shirinsa na lashe zaben jihar da za a gudanar Asabar mai zuwa.
Asali: Legit.ng