Muhimman Abubuwa 10 game da Zaben Gwamnan Jihar Ondo
- A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba hukumar zabe mai zaman kanta za ta gudanar da zaben gwamna a Ondo
- Yan takara daga jam'iyyu daban daban ke shirin karawa da gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa da yake jam'iyyar APC
- A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa a kan zaben jihar Ondo da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Biyo bayan zaben gwamna a jihar Edo, hukumar INEC za ta kara gudanar da zabe a jihar Ondo.
A ranar Asabar mai zuwa hukumar INEC za ta gudanar da zaben Ondo a kananan hukumomi 18 da ke jihar.
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani a kan zaben Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Yadda aka kirkiro jihar Ondo
Rahoton Premium Times ya nuna cewa a shekarar 1976 shugaban mulkin soja, Janar Murtala Muhammad ya kirkiro jihar Ondo.
Tun daga lokacin aka cigaba da damawa da jihar a bangaren siyasa, tattalin arziki da kasuwanci a Najeriya.
2. Yan takarar gwamna a zaben Ondo
Yan takara 17 ne za su kara a zaben da za a gudanar a jihar Ondo a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC zai kara da yan takarar a yayin da yake neman tazarce.
3. Manyan yan takara a Ondo
Manyan yan takara a zaɓen Ondo na 2024 sun hada da gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC da Ajayi Agboola na PDP.
Haka zalika akwai Otumba Bemidele Akingboye na jam'iyyar SDP da Sola Ebiseni na jam'iyyar LP.
4. Kananan hukumomin Ondo
Jihar Ondo nada ƙananan hukumomin 18 kuma a cikinsu za a gudanar da zaben ranar Asabar mai zuwa.
Rahoton Legit ya nuna cewa an raba ƙananan hukumomin zuwa Ondo ta Arewa, Ondo ta Kudu da Ondo ta Tsakiya.
5. 'Yan takaran APC da PDP sun fito daga yanki 1
Rahotanni sun nuna cewa dukkan manyan yan takarar jam'iyyar PDP da APC sun fito daga yankin Ondo ta Kudu.
Gwamna jihar, Lucky Aiyedatiwa yana wakiltar APC yayin da Ajayi Agboola ke wakiltar jam'iyyar PDP.
6. Gwamna 1 da ya kammala wa'adinsa a Ondo
Tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko ne kawai ya taba yin wa'adi biyu a kan karagar mulkin jihar Ondo.
Kotun tarayya ta tabbatar da Mimiko a matsayin gwamnan Ondo a 2007 kuma ya samu mulki karo ba biyu a 2012.
Gwamna Rotimi Akeredolu ya samu nasarar zabe karo na biyu amma bai samu cika wa'adin mulkin ba ya rasu a 2023.
7. Sanadin samun mulkin Aiyedatiwa
Bayan mutuwar gwamna Rotimi Akeredolu a 2023, mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa ya zama gwamna.
A yanzu haka dai Lucky Aiyedatiwa zai nemi mulki a 2024 bayan ya cika wa'adin Rotimi Akeredolu.
8. Tsofaffin gwamnoni sun rasu
Jihar Ondo ta kasance jihar da dukkan tsofaffin gwamnoninta suka rasu illa Olusegun Mimiko kawai.
Bayan kafa tarihin mulki sau biyu, Mimiko ya kara zama tsohon gwamnan jihar da yake cigaba da rayuwa a duniya.
9. Jam'iyyun da suka yi mulki a jihar Ondo
Jam'iyyun siyasa shida ne suka yi mulki a jihar Ondo tun bayan kafa jihar a 1976.
- UPN daga 1979 zuwa 1983
- SDP daga 1992 zuwa 1993
- AD daga 1999 zuwa 2003
- PDP daga 2003 zuwa 2009
- LP daga 2009 zuwa 2017
- APC daga 2017 zuwa yau
10. Mummunan rikicin zaɓe
A shekarar 1983 aka samu mummunan rikicin zaɓe a jihar Ondo da ya jawo kone kone a fadin jihar.
Jaridar Punch ta wallafa cewa an fara rikicin ne bayan hukumar zabe ta sanar da cewa Akin Omoboriowo ne ya yi nasara.
Ondo: Ganduje ya ce APC za ta ci zabe
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa ya bukaci mutanen Ondo da su hada kai wajen zaben gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Haka zalika, shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce suna da tabbas a kan cewa za su lashe zabe a dukkan kananan hukumomin Ondo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng