Zaben Ondo: Abubuwan Sani Dangane da Sola Ebiseni, 'Dan Takarar LP
- Jihar Ondo na shirin zaɓen gwamna wanda zai ja ragamarta zuwa nan da shekara huɗu masu zuwa
- Ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP), Sola Ebiseni na daga cikin mutanen da ke son al'ummar jihar Ondo su ɗamka musu ragamar shugabanci
- Sola Ebiseni ƙwararren lauya ne wanda ya rikiɗe zuwa harkokin siyasa domin ba da ta sa gudunmawar wajen kawo cigaba a cikin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Sola Ebiseni na jam'iyyar LP na daga cikin ƴan takarar da ake yi wa kallon za su kai labari a zaɓen gwamnan jihar Ondo.
A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba ne dai za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo.
Abubuwan sani a kan Sola Ebiseni
Legit.ng ta tattaro muhimman abubuwa guda bakwai game da Sola Ebiseni da ya kamata ku sani:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Karatun Sola Ebiseni
Sola Ebiseni ya yi digirinsa na farko a fannin shari'a (BL, LLB) a jami'ar Ife da ke da dinbin tarihi a Najeriya.
Mai neman zama gwamnan ya zama lauya a shekarar 1986 inda daga nan ne ya fara aikinsa a fannin shari'a.
2. Aikin da yake yi
Sola Ebiseni ya kasance lauya kuma abokin hulɗa a Ebisen da Oropato Chambers tun shekarar 1987.
Kwarewar da yake da ita a fannin shari'a ta taka muhimmiyar rawa kan abin da ya zama a rayuwarsa.
3. Gogewar Sola Ebiseni a siyasa
Labarin siyasar Sola Ebiseni ya fara ne a shekarar 1989 lokacin da ya zama shugaban ƙaramar hukumar Ilaje Eze Odo a jihar Ondo.
Daga nan ya riƙe mukamai daban-daban da suka haɗa da kwamishinan muhalli da ma’adanai a jihar Ondo tun a shekarar 2002.
4. Muƙaman shugabanci da ya riƙe
Baya ga harkokin siyasa da shari’a, Sola Ebiseni ya riƙe mukamin daraktan kamfanin Oluwa Glass da ke Gbokada tun a shekarar 1999.
Ɗan takarar na Labour Party ya riƙe muƙamai na jagoranci a sassa daban-daban.
5. Takara a jam'iyyar LP a zaben Ondo
Shugabannin jam’iyyar LP na ƙasa sun ayyana Sola Ebiseni a matsayin ɗan takararsu na zaɓen gwamnan Ondo.
Samun takararsa ya biyo bayan janyewar tsohon ɗan takarar jam’iyyar a baya wanda ba bakon abu ba ne a siyasa.
6. Manufofinsa kan mulki
Sola Ebiseni ya himmatu wajen yin amfani da muhimman abubuwan da marigayi Cif Obafemi Awolowo ya maida hankali a kai wajen gudanar da mulki.
Ɗan takarar ya yi alƙawarin maida da hankali wajen ba da ilimi kyauta, kiwon lafiya kyauta, samar da ayyukan yi da raya karkara, cewar rahoton jaridar The Punch.
Gwamnan Ondo ya ba da hutun zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Ondo ta ayyana ranar hutu domin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa ta ayyana ranar Juma’a 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng