Shiga Ofis Ke da Wuya, Gwamna Ya Rushe Ma'aikata, Ya Rufe Asusun Kudin Jihar

Shiga Ofis Ke da Wuya, Gwamna Ya Rushe Ma'aikata, Ya Rufe Asusun Kudin Jihar

  • Kwana biyu da shiga ofis, Gwamna Monday Okpebholo ya rushe wata ma'aikata da gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira
  • Gwamna Okpebholo ya kuma umarci rufe asusun jihar da ke dukan bankunan yan kasuwa har sai an kammala bincike
  • Gwamnan ya kuma yi gargadi ga bankunan da sauran masu jagorantar ma'aikatu a jihar su bi umarnin sau da kafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya fara daukar wasu matakai masu tsauri domin daidaita jihar.

Gwamna Monday Okpebholo ya umarci rufe dukan asusun jihar da ke bankuna daban-daban a jihar nan take.

Gwamna ya umarci rufe dukan asusun bankunan jiharsa
Gwamna Monday Okpebholo ya rushe ma'aikatar hanyoyi da gadaje. Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun.
Asali: Facebook

Gwamna Okpebholo ya gargadi shugabannin ma'aikatu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sakataren yada labaransa, Fred Itua ya fitar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kori hadimai da shugabannin hukumomi, ya umarci kowa ya bar ofis

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Itua ya ce Gwamna Okpebholo ya gargadi dukan shugabannin hukumomi da ma'aikatu da kuma bankuna su bi umarnin ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan ya ce duk wanda aka samu da bijirewa dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani.

"Dukan asusun bakunan jihar an rufe su, ina umartan bakunan su bi umarnin tabbatar da cewa ba a fitar da ko sisin kwabo ba har sai bayan fitar da sanarwa."
"Shugabanni ma'aikatu da hukumomi su tabbatar sun bi umarnin ba tare da bata wani lokaci ba."
"Bayan kammala bincike gwamnan zai yi duba kan hanyar bullowa lamarin amma a yanzu umarnin ta tabbata."

- Fred Itua

Gwamna ya rushe ma'aikatar da Obaseki ya kirkira

Har ila yau, Gwamna Okpebholo ya umarci rushe ma'aikatar hanyoyi da gadaje da gwamnatin Godwin Obaseki ta kirkira, Tribune ta ruwaito.

Okpebholo ya umarci hada ma'aikatar da ta ayyuka inda ya ce babu wata hanya ko gada da Obaseki ya yi, saboda haka sunan bai da amfani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda gwamnati ta tunkari matsalar tattalin arziki gaba gadi

Sabon gwamna ya kori masu rike da mukamai

Kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya kori dukkan shugabannin hukumomi da masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar Edo.

Okpebholo ya ɗauki wannan mataki ne sa'o'i 24 bayan karɓar rantsuwar kama aiki a matsayin sabon gwamnan Edo.

Gwamnan ya kuma dakatar da tattara kuɗin shiga musamman a tasoshin mota, ya ce nan gaba kaɗan zai sanar da sabon tsari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.