'Tinubu bai Tanadi Komai ga Najeriya ba,' Atiku ya Tono Wani Sirri
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya sake dura kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Atiku Abubakar ya ce alamu sun nuna cewa Bola Tinubu bai yi shirin komai ga yan Najeriya ba shi ya sa abubuwa suka rikice
- Martanin Atiku ya zo ne bayan fadar shugaba kasa ta ce yana yi wa Bola Tinubu hassadar samun nasara a zaben 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi martani mai zafi ga Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu ya karbi mulki ne ba tare da wata manufar kawo cigaba a Najeriya ba.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa Atiku Abubakar ya ce bai ga abin da zai saka ya yi hassada ga Tinubu a kan azaba da yake ganawa yan Najeriya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya ce Tinubu bai shirya mulki ba
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu bai shirya komai a kan mulkin Najeriya ba.
Rahoton Arise News ya nuna cewa Atiku Abubakar ya ce rashin shirin ne ya sanya Bola Tinubu cire tallafin man fetur kafin shiga ofis.
Bayan haka, Atiku ya ce da Tinubu ya rasa yadda zai yi sai ya kawo maganar motocin CNG duk da cewa babu gidajen man su a Najeriya.
Atiku ya ce ba ya hassada ga Tinubu
Atiku Abubakar ya ce bai ga wani abin kirki da Bola Tinubu yake yi a Najeriya ba balle ya yi masa hassada ba.
A cewar Atiku, a ranar 8 ga Yuli Tinubu ya yi alkawarin shigo da kayan abinci ba tare da haraji ba na kwanaki 150 amma dokar ba ta fara aiki ba bayan kwanaki 120.
"Rashin tausayi ya zamo siffar Tinubu. Ba wani shugaban da zai yi hassada ga wanda yake gallazawa yan Najeriya.
Bai kama hankali ba a ce Atiku na yi wa Tinubu hassada. Atiku ba zai yi hassada ga mai saka mutane a wahala ba."
- Atiku Abubakar
Sarakuna sun bukaci kawo saukin rayuwa
A wani rahoton, kun ji cewa sarakunan gargajiya a jihar Delta sun yi magana da murya daya ga gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan halin wahalar rayuwa da ake ciki.
Mai magana da yawun sarakunan, Luke Kalanama VIII ne ya zanta da manema labarai bayan sun yi taro a masarautar Akugbene-Mein.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng