Jam'iyyu na Shiri, INEC Ta Kai Kayan Zaben Gwamnan Jihar Ondo

Jam'iyyu na Shiri, INEC Ta Kai Kayan Zaben Gwamnan Jihar Ondo

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa ta fara kai muhimman kayan gudanar da zaben Ondo jihar
  • Hukumar INEC ta ba mazauna Ondo ranar 16 Nuwamba, 2024 domin su zabi wanda zai jagorance su a matsayin gwamna
  • A sanarwar da hukumar zabe ta fitar, an kai kayan zaben a ranar Litinin kuma an damka su ga jami'an babban bankin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo – Kayan zabe masu muhimmanci sun isa Akure a jihar Ondo yayin da jam’iyyu ke shirin tunkarar zabe mai zuwa.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanya ranar 16 Nuwamba domin gudanar da zaben gwamna a jihar,

Zaben Ondo
INEC ta kai kayan zabe jihar Ondo Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

A sanarwar da hukumar INEC ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa an yi jigilar kayan ne domin kara karfafa shirin zaben.

Kara karanta wannan

Jigo ya tsallake Kwankwaso, Atiku, ya fadi wanda zai karbi mulki hannun Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar INEC ta kai kayan zabe jihar Ondo

Jaridar Punch ta wallafa cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa jirgin saman rundunar sojin saman Najeriya ce ta kai kayan zaben Ondo.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce tuni jami’an babban bankin kasa (CBN) su ka karbi kayan a Akure, babban birnin jihar.

INEC na shirin gudanar da zaben Ondo

Hukumar zaben kasar nan ta bayyana cewa an fara kai kayan zabe jihar Ondo ne domin tabbatar da ana zaune cikin shiri.

Za a gudanar da zaben a ranar 16 ga Nuwamba inda kowace jam’iyya daga APC, PDP da NNPP ke ganin ita ce za ta yi nasarar samun kujerar.

Yan sanda za su tura jami’ai zaben Ondo

A baya mun ruwaito cewa Sufetan yan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun ya yi takaicin yadda yan siyasa ke kawo tarzoma yayin gudanar da zabe kuma haka na zama barazana.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da Tinubu ya isa birnin Riyadh, zai halarci manyan tarurruka 2

Sufetan yan sandan ya bayyana cewa haka ta sa za a tura jami’ai akalla 22,239 tare da aiki da sauran hukumomin tsaro domin ganin an gudanar da zaben Ondo lafiya kuma cikin adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.