Obasanjo Ya Magantu kan Jam'iyyar Siyasa da Yake, Ya Shawarci Yan Najeriya
- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce kwata-kwata bai da wata jam'iyyar siyasa da yake goyon baya
- Cif Obasanjo ya bayyana cewa shi a yanzu bai da jam'iyya yana nan a matsayin dan kasa da bai da alaka da jam'iyyar siyasa
- Tsohon shugaban kasar ya koka kan yadda yan kasa ke fuskantar matsaloli daban-daban inda ya ce akwai haske a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan jam'iyyun siyasa a Najeriya.
Obasanjo ya ce babu wata jam'iyyar siyasa a Najeriya da yake so ko goyon baya a halin yanzu a kasar.
Obasanjo ya koka kan halin kunci a Najeriya
Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya fadi haka ne a Abuja yayin bikin ranar haihuwar tsohon shugaban NDDC, Onyema Ugochukwu, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda yan Najeriya ke fuskantar matsaloli a kasar da suka ki ci suka ki cinyewa.
Sai dai Obasanjo ya roki al'ummar Najeriya da su cigaba da saka rai da fatan za a samu sauki a gaba.
Obasanjo ya yabawa Onyema Ugochukwu kan dogewarsa
Obasanjo ya yabawa Onyema Ugochukwu da ya cika shekaru 80 a duniya inda ya ce mutum ne mai biyayya da taimako.
"Lokacin da muka hadu daf da kamfe na 1999, na sanka ne saboda irin kyawawan halayenka."
"Duk da muna takara da Alex Ekweme tun farko ka zabi wanda za ka bi, duk da ba ni da wata jam'iyya a yanzu, amma na san zan iya dogaro da kai a kowane lokaci."
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya yabawa matarsa lokacin da yake kulle
Kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya kara yabawa matarsa, Marigayiya Stella Obasanjo a wurin bikin ƙaddamar da asibitin da aka raɗawa sunanta.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana yadda Stella ta shiga ta fita, ta karaɗe manyan ƙasashe a duniya domin a sako shi daga gidan yari.
Obasanjo ya yi zaman gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha amma daga bisani ya fito kuma ya lashe zaɓen shugaban kasa.
Asali: Legit.ng