Ana Shirin Rantsar da Sabon Gwamnan Edo, Jam'iyyar APC Ta Hango Matsala

Ana Shirin Rantsar da Sabon Gwamnan Edo, Jam'iyyar APC Ta Hango Matsala

  • Jam'iyyar APC ta nuna damuwa kan wasu naɗe-naɗe da gwamnan Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya yi kwanan nan
  • APC ta yi zargin cewa Obaseki ya dawo da wasu tsofaffin hadimansa kuma ya ɗauki wasu aiki da nufin yi wa sabon gwamna mugunta
  • Sai dai gwamnatin Edo ta maida martani da cewa ya kamata APC ta kama bakinta, ta maida hankali wajen sharin karɓar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta caccaki Gwamna Godwin Obaseki mai barin gado bisa wasu matakai da yake ɗauka ana dab da rantsar da sabon gwamna.

APC ta nuna ɓacin ranta kan matakin Obaseki ya ɗauka na dawo da wasu tsofaffin hadimansa bakin aiki da kuma naɗa wasu masu taimaka masa.

Kara karanta wannan

Bayan sauke masu mukamai a gwamnati, gwamna ya fallasa shirin APC

Godwin Obaseki.
APC ta soki matakan da gwamna mai barin gado a jihar Edo ya ɗauka ana dab da rantsar da zababben gwamna Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Jam'iyyar ta ce gwamnan yana haka ne da nufin mugunta ga zababben gwamna mai jiran gado, Monday Okpebholo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban APC na jihar Edo, Jarrett Tenebe ya fitar ranar Juma'a.

APC ta zargi Obaseki da gina ramin mugunta

"APC ta ji ƙishin-ƙishin cewa gwamna mai barin gado yana ɗaukar wasu matakai yayin da wa'adinsa ya zo gargara, da muka bincika mun gano cewa labarin akwai ƙanshin gaskiya.
"Mun gano shirinsa na dawo da da ɗaruruwan tsofaffin hadimansa bakin aiki da ɗauko ma'aikatan kanfaminsa Afrinvest ya ba su aiki a gwamnati saboda mugunta.
"Bisa haka muna sanar da al'ummar Edo cewa matakin da Obaseki ke ɗauka na karawa gwamnati nauyi ya saɓa rantsuwar da ya yi kuma zagon ƙasa ne ga tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Abinci ya kare: Gwamna ya rusa dukan masu mukamai a gwamnatinsa, ya yi godiya

- Jarrett Tenebe.

Gwamnatin Obaseki ta yi martani

Da yake martani, kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Chris Nehikhare ya buƙaci APC ta daina ƙorafi, ta shirya shugabancin al'umma.

Ya ce ko da sun taras da bautul-mali ba ko kwandaga idan sun karɓi mulki, bayan kwanaki kaɗan asusun tara kudin shiga da kasafi zai aiko da kason Edo na wata, rahoton Vanguard.

Gwamna Obaseki ya sallami muƙarrabansa

A wani labarin, an ji cewa kwanaki ƙadan kafin barin mulki, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai.

Obaseki ya dauki matakin ne yayin da yake kwanakin karshe na wa'adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar Edo da ke Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262