Zaben Amurka: Jam'iyyar Republican Ta Lashe Manyan Kujerun Majalisar Dattawa

Zaben Amurka: Jam'iyyar Republican Ta Lashe Manyan Kujerun Majalisar Dattawa

  • Jam'iyyar adawa ta Republican ta lashe manyan kujeru a majalisar dattawa kuma da alama ita ke kan gaba da a zaben ƴan majalisar Amurka
  • Hakan na nufin Republican na shirin karbe shugabancin majalisar dattawa a Amurka bayan lashe kujerun sanatoci a Ohio da West Virginia
  • Waɗannan kujeru dai na da matukar muhimmanci kuma suna taka rawa ga shugaban ƙasa wajen cimma manufofinsa a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States - Ga dukkan alamu jam'iyyar Republican na shirin karbe ragamar majalisar dattawan ƙasar Amurka daga hannun ƴan Democrats karo na farko a shekaru huɗu.

Rahotanni sun nuna Republican ta lashe manyan kujerun ƴan majalisa a jihohin Ohio da Yammacin Virginia ranar Talata, 5 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Abubuwan da suka jefa mutane cikin yunwa da mafitarsu a Najeriya

Yan jam'iyyar Republican a Amurka.
Jam'iyyar Republican ta lashe kujeru mafi rinjaye a majalisar dattawan Amurka Hoto: Donald J. Trump
Asali: Facebook

Shafin ƴan jam'iyyar Republican a X ya yi ikirarin samun nasara a wani sako da ya wallafa bayan zaɓe ya kankama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ƴan majalisar sun samu mafi rinjayen kujeru a zaɓen da aka yi, hakan na nufin za su karɓe shugabancin majalisar Amurka.

Republican na shirin karbe shugabancin majalisa

Da wannan nasara da ƴan Republican ke hange, ƴan DOP ne za su karɓi jagoranci musamman da shugaban majalisar Amurka na yanzu, Mitch McConnell ya sanar da shirinsa na yin murabus.

Ana sa ran shugaban masu rinjaye na majalisar Amurka na yanzu, dan Democrat Chuck Schumer na jihar New York, shi ne zai zama shugaban marasa rinjaye.

Wannan canji na zuwa ne bayan nasarar da jam'iyyar Republican mai adawa ta samu na lashe kujeru biyu, ɗaya a Ohio, sai kuma a West Virginia.

Yadda jam'iyyar Republican ta ci manyan kujeru

Kara karanta wannan

"Za a zage ku," Abin da Tinubu ya faɗawa sababbin Ministoci bayan rantsar da su

Dan takarar Republican, Bernie Moreno ya yi nasara a Ohio, inda ya kori ɗan majalisa mai ci, Sherrod Brown na Democrat, a cewar rahoton NBC.

Haka nan kuma gwamnan jam'iyyar Republican, Jim Justice na jihar West Virginia ya samu nasarar lashe kujerar sanata da ɗan Democrat ke riƙe da ita.

Sanata Ted Cruz na jihar Texas shi ma dan jam'iyyar Republican ya doke abokin karawarsa a wata fafatawa mai zafi, yayin da Angela Alsobrooks ta Democrat ta lashe zabe a Maryland.

Sakamakon wadannan manyan kujerun ƴan majalisa za su taka rawar gani wajen baiwa shugaban kasa damar cimma muhimman manufofinsa kafin tsakiyar wa'adi a 2026.

Trump ya fara hango nasara a zaɓen Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fara zarra a zaben da Amurka ke gudanarwa, inda ya yi nasara a manyan jihohi shida.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya yi rashin hadimi, wani ɗan sanda ya rasu

Wannan na nufin akwai babbar barazana na yiwuwar Kamala Haris ta zama shugabar Amurka mace ta farko a tarihi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262