Kwankwaso na cikin Rigima a Kano, Dan Takara a NNPP Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

Kwankwaso na cikin Rigima a Kano, Dan Takara a NNPP Ya Shiga Tsaka Mai Wuya

  • 'Dan takarar jam'iyyar NNPP a zaben jihar Ondo, Gbenga Edema bai san makomarsa ba duk da daura kwanaki 11 zaɓe
  • Hakan ya biyo bayan shigar da korafi kan dan takarar a gaban Babbar Kotun jihar game da sahihancin shiga zaben gwamna
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Kwanaki kadan kafin zabe, dan takarar gwamnan jihar Ondo a NNPP bai san makomarsa ba.

Gbenga Edema ya tsaya takara ne a zaɓen da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Ba a gama da Kano ba, gwamnatin Zulum ta gurfanar da kananan yara da wasu 16

Har yanzu dan takarar gwamna a NNPP bai san makomarsa ba a zabe
Dan takarar gwamna a Ondo karkashin NNPP yana jiran makomarsa ana daf da zabe. Hoto: Olugbenga Edema.
Asali: Facebook

Dan takarar NNPP na jiran tsammani a jihar Ondo

Tribune ta ce har zuwa yanzu Edema bai san makomarsa ba saboda kotu ba ta yanke hukunci kan sahihin dan takarar jam'iyyar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan korafin wasu a jam'iyyar NNPP kan dan takarar a ranar 12 ga watan Agustan 2024.

Daga cikin masu korafin akwai Injiniya Akintan Michael da Mrs Kemi Fasua da Dakta Gilbert Major Agbo da Comrade Oginni Olaposi.

Korafe-korafe kan dan takarar NNPP a Ondo

Ana korafin ne kan abubuwa guda biyu da suka shafi mika sunayen mambobin jam'iyyar wata daya kafin gudanar da zaben fitar da gwani.

Sannan akwai korafi kan kokwanton kasancewar dan takarar a cikin jerin mambobin jam'iyyar har zuwa ranar zaben fitar da gwani.

A Babbar Kotun jihar Ogun da ke Akure, Mai Shari'a, Oluyemi Akintan Osadabay ya saurari dukan korafe-korafen bangarorin, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi martani ga Atiku, ta fadi abin da zai faru idan da PDP ke mulki

Daga bisani alƙalin kotun ya daga cigaba da sauraran shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Nuwambar 2024.

Edema ya samu takara a NNPP

Kun ji cewa Barista Olugbenga Edema ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Ondo a inuwar NNPP bayan ya baro jam'iyyar APC.

Tsohon jigon jam'iyya mai mulki ya ce ya shirya sauke Gwamna Lucky Aiyedatiwa daga mulki a zaɓen watan Nuwamba, 2024.

NNPP ta ba Edema tikitin takara ne bayan tsohon ɗan takararta, Oluwatosin ya janye daga takara bisa ra'ayin kansa da kishin jam'iyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.