A Karshe, Hukumar INEC Ta Yi Magana kan Rikicin Majalisar Dokokin Jihar Ribas
- Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana cewa ta rasa yadda za ta yi da rikicin majalisar dokokin jihar Ribas
- Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ya ce kowane ɓangare ya buƙaci a maye gurbin abokan hamayyarsa, sannan kuma kotuna na cin karo da juna
- Farfesa Mahmud ya ce a halin yanzu dai INEC na bibiyar abubuwan da ke faruwa a majalisar amma ba za ta iya yin komai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, a ranar Juma’a, ta bayyana matsayarta kan rikicin da ke faruwa a majalisar dokokin jihar Ribas.
Hukumar INEC ta ce tun farko ta yi shiru saboda yadda hukuncin kotuna ke cin karo da juna, ta rasa wanda za ta ɗauka.
Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya faɗi haka da yake jawabi a wani taro a hedkwatar hukumar da ke Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane rikici ake yi a majalisar Ribas?
Tsagin majalisar dokokin Ribas mai goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya buƙaci INEC ta shirya zaben maye gurbin ƴan majalisa 25 na tsagin Nyesom Wike.
Haka a ɗaya bangaren ƴan majalisar tsagin Wike sun ayyana kujerun abokan hamayyarsu a matsayin babu kowa, ma'ana INEC ta cike gurbinsu.
Da yake martani kan kiraye-kirayen INEC ta shiga tsakani, Mahmud Yakubu ya ce hukuncin kotuna masu cin karo da juna a matakin jiha da tarayya ya jefa INEC cikin ruɗani.
INEC ta yi magana kan rikicin majalisar
Ya ce a yanzun INEC ta rasa wane hukunci za ta ɗauka kuma ba ta da tabbacin su waye halastattun ƴan majalisar dokokin jihar Ribas.
Premium Times ta ruwaito Mahmud Yakubu na cewa:
"Ƴan majalisa uku sun ayyana kujerun abokan aikinsu 25 da babu kowa, haka su ma ƴan majalisa 25 sun ce a maye gurbin mambobi uku. Bayan haka kotun jiha da ta tarayya sun ce kowane bangare yana da gaskiya.
"Hukumar zaɓe INEC na bibiyar duk abin da ke faruwa, ba mu san ya za ta kaya ba nan gaba, don haka muna sojin jin ra'ayoyin ƴan Najeriya musamman masana shari'a."
Fubara ya taɓo sulhun Shugaba Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan zaman sulhu da shugaban Bola Tinubu ya yi tsakaninsa da Nyesom Wike.
Siminalayi Fubara ya zargi Nyesom Wike da karya sharudan da aka gindaya yayin zaman sulhun da suka yi a fadar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng