Sanatan NNPP Ya Ba Ƴan Majalisa Dariya a Lokacin Tantance Sabon Minista daga Kano
- Sanatan Kano ta tsakiya, Rufai Hanga ya ce naɗa Yusuf Abdullahi Ata a matsayin minista tamkar barazana ce a gare shi
- Rufai Hanga na jam'iyyar NNPP ya yabi sabon ministan, inda ya ba abokan aikinsa dariya saboda kalaman da ya faɗa
- Haka nan Kawu Sumaila ya bayyana sabon ƙaramin ministan a matsayin ɗan siyasa na asali da ke da kusanci da jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sanata Rufai Hanga ya ba sanatoci dariya a lokacin tantance sabon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata.
Sanatocin sun barke da dariya ne a lokacin da Sanata Hanga ya ce naɗin Yusuf Ata a matsayin minista barazana ce a gare shi, ya faɗi hakan ne cikin barkwanci.
Tun farko shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya buƙaci Sanata Rufa'i Hanga na NNPP ya yi tsokaci kan sabon ministan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan Kano ya bada dariya a majalisa
Da yake tsokacin kamar yadda aka nema, Sanata Rufai, ɗan jam'iyyar NNPP ya ce:
"Naɗin wannan jigon siyasar barazana ce a gare ni saboda ɗan mazaɓata ne, shi ɗan siyasa ne kuma abokina, hakan na nufin ina goyon naɗinsa."
Sai dai Akpabio ya shaidawa Sanata Rufai Hanga cewa babu wani abin damuwa ya kwantar da hankalinsa, inda ya kira shi da mutumin kirki kuma wanda ya iya zama da mutane.
"Duk da banbancin jam'iyyar siyasa, amma kun haɗu wuri ɗaya kuna goyon bayan sabon ministan," in ji Akpabio.
Kawu Sumaila ya yabi Yusuf Abdullahi Ata
Tun da farko, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila (NNPP, Kano ta Kudu) ya bukaci abokan aikinsa da su bar sabon ministan ya rusuna kawai ya wuce.
Sanata Kawu ya bayyana cewa Yusuf Ata tsohon ɗan majalisa ne a Kano wanda ya rike kujerar kakakin majalisar dokokin jihar.
Kawu Sumaila ya bayyana Yusuf Ata a matsayin dan siyasa na kusa da jama'a wanda ya fara siyasa tun daga tushe kuma yana da kyakkyawar alaka da al'umma.
Sanata Barau ya ce APC za ta karɓe Kano
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Barau I. Jibrin ya ce jam'iyyar APC na shirin karɓe mulkin jihar Kano a babban zaɓe mai zuwa a 2027.
Mataimakin shugaban majalisar ya faɗi haka ne a lokacin da ake tantance sabon ƙaramin ministan gidaje da raya birane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng