APC Ta Yi Kamu, Mataimakiyar Dan Takarar Gwamna Ta Dawo Jam'iyyar

APC Ta Yi Kamu, Mataimakiyar Dan Takarar Gwamna Ta Dawo Jam'iyyar

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya karbi wata kusa a jam'iyyar SDP ana daf da gudanar da zaɓe
  • Gwamnan ya karbi mataimakiyar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Susan Gbemisola Alabi ana shirin zaɓe
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Nuwambar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Ana shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo, jam'iyyar APC ta yi babban kamu.

Mataimakiyar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Susan Gbemisola Alabi ta watsar da jam'iyyarta.

APC ta yi babban kamu ana daf da gudanar da zabe
Mataimakiyar dan takarar gwamna a Ondo ta koma APC a Ondo. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

Musabbabin dawowar kusa a PDP zuwa APC

Vanguard ta ce Susan ta yi murabus ne daga SDP a kwanakin bayan kan matsalarta dan takarar gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar PDP, jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Susan ta samu matsala da Otunba Bamidele Akingboye kan wasu matsaloli da suka gagara shawo kansu.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa shi ya karbi Alabi yayin kamfe a karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yammacin jihar.

Aiyedatiwa ya ba da tabbacin samar da abubuwan cigaba ga dukkan yankunan jihar domin cire su a kangin da suke ciki.

Ya godewa sarakunan gargajiya kan irin goyon baya da suka ba shi musamman yayin zaben fitar da gwani, cewar rahoton The Nation.

Gwamna ya sha alwashin kawo sauyi a jihar

"Zuwa na nan da kai na na gano abubuwan da kuke bukata ba sai an fada ba."
"Zan yi iya bakin kokari na wurin samar da cigaba musamman a ɓangarorin da ke da matsala a cikin al'umma."

- Lucky Aiyedatiwa

Gwamna Aiyedatiwa ya sha alwashin tafiya tare da dukan al'ummar jihar ba tare da wariyar jam'iyya ko bangaranci ba, ya ce dukan yan Ondo yayansa ne.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi, ya bada umarnin rufe makaranta bayan mutuwar wani ɗalibi

Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon gwamna

A baya, mun baku labarin cewa jam'iyyar APC a jihar Osun ta dakatar da tsohon gwamna, Ogbeni Rauf Aregbesola.

Jam'iyyar tana zargin tsohon Ministan a mulkin Muhammadu Buhari da cin amanar APC da wasu zarge-zarge.

Wannan na zuwa ne bayan mika takardar korafi kan tsohon gwamnan ga shugaban APC ta kasa, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.