Zaman Doya da Manja: Atiku Ya Magantu Kan Rikicin PDP, Ya Fadi Matsayarsa

Zaman Doya da Manja: Atiku Ya Magantu Kan Rikicin PDP, Ya Fadi Matsayarsa

  • Atiku ya ce bai da alaka da kowanne rikici da ke tattare da jam’iyyar ta kowacce fuska a halin yanzu
  • Jam’iyyar PDP na ci gaba da fuskantar rikice-rikice na cikin gida, mambobi na samun sabani da yawa
  • Har yanzu ana ci gaba da zaman doya da manja tsakanin Atiku Abubakar da ministan FCT, Nyesom Wike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 na PDP ya ce bai da hannu a kitimurmurar da ke aukuwa a jam’iyyar tasu.

Wannan na fitowa daga bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Phrank Shuaibu, inda yace Atiku bai da hannu a kusa ko nesa game da abin da ke faruwa a PDP.

Ya magantu kan batun rikicin PDP
Atiku ya ce bai da hannu a cikin PDP | Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, jam’iyyar na fuskanci rikice-rikice a cikin ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya kai ga sa bakin kungiyar gwamnoni ta jam’iyyar har da kwamitin amintattu don tabbatar da an daidaita lamurra.

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Zaman doya da manja tsakanin Atiku da Wike

Masu sharhi na bayyana cewa, rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar ba za su rasa nasaba da zaman doya da manja da ake yi tsakanin ministan FCT, Nyesom Wike da Atiku ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata tattaunawa da aka yi ranar Alhamis ta masu ruwa da tsaki na PDP, ba a gayyaci Atiku da Wike, lamarin da ke nuna da walakin; goro a miya.

Ana kuma fargabar cewa, akwai yiwuwar jam’iyyar ta sake samun bayyanar baraka tsakanin manyan mambobinta a wani zaman NEC da za ta yi a ranar 28 ga watan Nuwamba,

Sai dai, da aka tambayi shi tsagin Atiku na hannu game da yadda wasu mabobin PDP suka yi hayar lauyoyi a wata kitimurmurar jam’iyyar, Shuaibu ya ce sam babu alama.

Halin rikici da PDP ke ciki

Kara karanta wannan

'Kirista dan Kudu,' Tsagin PDP ya fadi wanda zai shiga takara a 2027

A baya kadan, wasu mambobin PDP sun shigar da kara kan cewa, a dakatar da duk wani batu da ke da alaka da tsige Ambasada Umar Damagum daga kujerarsa ta shugabancin jam’iyyar.

Tun kafin zaben shugaban kasa jam’iyyar PDP ke fuskantar rikicin cikin gida, inda tsagin Atiku da Wike ci gaba da zaman kishiyoyi.

Rikicin ya ci gaba da ruruwa zuwa yanzu, inda ake zargin Wike da rabar gwamnatin APC bayan da ya karbi kujerar minista a gwamnatin Bola Tinubu.

PDP ta amince Damagum ya sauka

A wani labarin, masu ruwa da tsaki sun wanda zai maye gurbin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum gabanin taron majalisar zartaswa watau NEC.

Jam'iyyar PDP ta shirya taron kwamitin zartaswa NEC wanda ke da alhakin zartar da hukunci musamman kan shugabanci a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Daily Trust ta tattaro cewa tuni kwamitin zartarwa na Arewa ta Tsakiya (ZEC) ya fara laluben wanda ya kamata ya karɓi shugabancin PDP daga shiyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.