Kano: Duk da Kotu Ta Taka Birki, Hukumar KANSIEC na Shirin Zaben Ranar Asabar
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kano (KANSIEC) ta hada gwiwa da Citizens for Development and Education don wayar da kan jama’a
- An gudanar da taron a wani shiri na zaben ranar Asabar da babbar kotun tarayya karkashin Mai Shari’a Simon Amobode ta haramta
- Shugaban kungiyar CDE ya sanar da jama’a muhimmancin zaben wanda su ke so, tare da jaddada masu muhimmancin zabe cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyar Citizens for Development and Education (CDE), da hadin gwiwar hukumar zabe mai zaman kanta sun shirya taro na musamman kan zaben kananan hukumomi a Kano.
An gudanar da taron da zummar nusar da jama’a muhimmancin zabe a cikin lumana a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro cewa hukumar KANSIEC ta ce an gudanar da taron a kokarinta na gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
KANSIEC ta wayar da kan masu zabe a Kano
Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta yi watsi da umarnin da kotu ta bayar, tare da ci gaba da gudanar da shirin tunkarar zaben kananan hukumomi.
Babbar kotun tarayya dai ta dakatar da hukumar KANSIEC daga gudanar da zaben ranar Asabar 26 Oktoba, 2024.
Kano: Abin da aka fadawa masu zabe
Shugaban kungiyar CDE, kuma shugaban masu sa ido kan zaben kananan hukumomi a Kano, Ambasada Ibrahim Waiya ya shawarci jama’ar su tabbata sun zabi shugabanni na gari.
Ambasada Waiya ta shaidawa Legit cewa za su yi tsayin daka wajen ganin an gudanar da zaben ba tare da samun matsala ba.
“Za a yi zabe a Kano:” Majalisa
A baya mun wallafa cewa majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu gudu babu ja da baya wajen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar wanda aka sa za a yi a ranar Asabar, 2 Oktoba, 2024.
Shugaban masu rinjaye na majalisa, Lawan Hussaini Dala ne jaddada matasayar gwamnatin Kano bayan babbar kotun tarayya ta dakatar da zaben tare da haramta nadin shugaban hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng