Gwamnoni da Jiga Jigai Sun Gano Abin da Zai Hana PDP Ƙwace Mulki daga Tinubu a 2027
- Gwamnoni da shugabannin PDP na kasa sun nuna damuwa kan rikicin cikin gida da ya ƙi karewa a babbar jam'iyyar adawar
- Sun ce matukar ba a binne duk wani saɓani ba, rikicin ka iya kawo cikas a kokarin PDP na komawa kan madafun iko a 2027
- Wannan na kunshe ne a sanarwa da gwamna Bala Mohammed, shugaban kungiyar gwamnonin PDP ya fitar bayan taronsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwammoni da masu ruwa da tsakin PDP sun yi gargaɗin cewa rigimar da ke faruwa a jam'iyyar ka iya wargaza shirinsu na karɓe mulki a zaɓen 2027.
Sun hango wannan matsala ne a taron da ya gudana karƙashin kungiyar gwamnonin PDP a Abuja ranar Talata da daddare.
Kamar yadda Leadership ta kawo, a wannan taron jam'iyyar PDP ta sake ɗage taron majalisar zartaswa watau NEC karo na biyu zuwa ranar 28 ga Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kusoshin PDP sun halarci taro da gwamnoni
Masu ruwa da tsakin PDP da suka halarci taron ranar Talata sun haɗa da kungiyar gwamnonin jam'iyyar da kwamitin amintattu watau BoT.
Sauran sun haɗa da kwamitin gudanarwa NWC, ƴan majalisar tarayya na jam'iyyar da ƙungiyar tsofaffin gwamnoni.
Sanarwa da aka fitar bayan taron ɗauke da sa hannun gwamnan Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Muhammed, ta nuna damuwa kan rikicin cikin gida.
Jam'iyyar PDP ta ɗauki matakin magance rikici
Sanarwar ta ce:
"A koƙarin haɗa kan ƴaƴan PDP da turmushe masu zagon ƙasa, jam'iyya ta buƙaci mambobinta su dunƙule wuri ɗaya, ka da su aminta da masu yunkurin ruguza jam'iyya.
"Taron ya kuma buƙaci ƴaƴan jam'iyyar su yi watsi da kalaman da ka iya raba kawunansu wanda za su iya gurgunta ƙoƙarin da ake na dawo da PDP kan turba da shirin karɓe mulki a 2027."
This Day ta ce PDP na fama da rikicin cikin gida musamman tsakanin tsagin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da ministan Abuja, Nyesom Wike.
Jigon PDP ya yi magana kan shugabancin jam'iyya
A wani rahoton kuma kun ji cewa ana ci gaba da shirye-shiryen wanda zai karɓi ragamar shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa daga hannun Umar Iliya Damagum.
Tsohon sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne zai samar da wanda zai canji Damagum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng