Bayan Tinubu Ya Kori Ministoci 5, Ɗan Takarar Gwamna Ya Dawo Jam'iyyar APC

Bayan Tinubu Ya Kori Ministoci 5, Ɗan Takarar Gwamna Ya Dawo Jam'iyyar APC

  • Jim kaɗan bayan korar wasu ministoci a gwamnatin Bola Tinubu, jam'iyyar APC ta samu karuwa a jihar Ribas
  • Tsohon kwamishinan Rotimi Amaechi kuma ɗan takarar gwamna na AA a 2023, Dr. Dawari George ya dawo APC
  • Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ƴan kwamitin NWC suka tarbi babban ɗan siyasar a sakatariyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dokta Dawari George, makusancin tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya koma jam’iyyar APC a hukumance ranar Laraba.

Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ne ya tarbi ɗan siyasar a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja.

Ganduje ya karbi tsohon kwamishinan Amaechi.
Tsohon kwamihinan Amaechi, George ya dawo jam'iyyar APC mai mulki Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jam'iyyar APC ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnoni da jiga jigai sun gano abin da zai hana PDP ƙwace mulki daga Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda George ya bar APC a 2022

George, wanda a baya ya rike mukamin kwamishinan makamashi da albarkatun kasa a gwamnatin Amaechi, ya bar APC zuwa jam'iyyar AA a 2022.

Ya kuma yi takarar gwamnan jihar Ribas karkashin inuwar jam'iyyar AA a babban zaɓen 2023 da ya gabata.

Lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya bar APC a 2022 ya koma AA, tsohon dan majalisar wakilan ya shaida wa manema labarai cewa yana yunwar yi wa jama'a aiki.

Ɗan takarar gwamna a 2023 ya dawo APC

Bayan dawowarsa APC, George ya samu kyakkyawar tarba daga Ganduje da ƴan kwamitin gudanarwa na kasa a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Tsohon dan takarar gwamnan bai yi magana da manema labarai ba bayan ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC.

Sanarwar da APC ta wallafa a shafin X ta ce:

Kara karanta wannan

'Kirista dan Kudu,' Tsagin PDP ya fadi wanda zai shiga takara a 2027

"Dr Dawari Ibietela George, dan takarar gwamnan jihar Ribas a zaben 2023 na jam'iyyar AA ya dawo inuwar APC.
"Ya samu tarba hannu bibbiyu daga shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sauran ƴan kwamitin gudanarwa a sakatariyar jam'iyya da ke Abuja."

Gwamna ya maida martani ga Ganduje

A wani labarin kuma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya mayar da martani ga shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje da Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Makinde ya ce PDP za ta ba Ganduje da Gwamna Aiyedatiwa mamaki a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262