Damagum Zai Sauka, An Gano Wanda Zai Iya Zama Sabon Shugaban PDP na Ƙasa

Damagum Zai Sauka, An Gano Wanda Zai Iya Zama Sabon Shugaban PDP na Ƙasa

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Marka na iya zama wanda zai maye gurbin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa
  • Rahotanni sun nuna wasu ƙusoshi sun fara tuntuɓar Mark amma ya fara nuna danuwa kan kararrakin da ke kotu kan rikicin PDP
  • Wata majiya ta ce ana ganin Mark zai iya warware rikicin da ke faruwa a PDP saboda alaƙarsa da kowane ɓangare a jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wasu kusoshin PDP na ci gaba da matsawa tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark domin ya nemi zama shugaban jam'iyya na ƙasa.

An tattaro cewa tsohon shugaban kasa da tsohon ministan tsaro na cikin jiga-jigan da suka dage David Mark ya karɓe ragamar shugabancin PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Daga karshe an fadi yankin da zai samar da shugaban jam'iyyar na kasa

David Mark.
Jiga-jigan PDP sun fara nuna wanda suke zo ya zama sabon shugaban PDP na kasa Hoto: @BukolaSaraki
Asali: Twitter

Wata majiya mai tsuhe ta shaidawa Leadership cewa tsohon shugaban ƙasar ya tsoma baki ne domin dawo da PDP cikin hayyacinta gabanin babban taro na ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

David Mark na iya zama shugaban PDP

Sai dai duk da Sanata David Mark bai nuna sha'awa ba amma ya fito ne daga shiyyar Arewa ta Tsakiya, wanda ake ganin daga nan za a zaɓo sabon shugaban PDP.

Ƴan PDP a Arewa ta Tsakiya sun jima suna kiraye-kirayen Umar Damagum ya yi murabus domin maye gurbinsa da ɗan yankin Iyorchia Ayu.

Tsoron da David Mark yake yi a PDP

Haka nan wata majiya da ke kusa da David Mark ta bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattawan yana taka-tsan-tsan da ƙararraki da ke gaban kotu.

A cewar majiyar kiran da ake yi wa tsohon sanatan na ya karɓi ragamar PDP ya fara karbuwa ta amma har yanzu yana fargabar rikicin da ya addabi jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Damagum: Gwamna a Arewa ya yi amai ya lashe kan shugabancin PDP na ƙasa

"Ko da ya amince ya karɓi ragama domin daidaita jam'iyyar, ba na tunanin zai yarda ya zama shugaban wani tsagi a PDP," in ji majiyar.

Jiga-jigan PDP sun fara tuntuɓar Sanata Mark

Wata majiyar kuma ta tabbatar da cewa tuni masu ruwa da tsaki suka fara tuntuɓar David Mark don ya karɓi shugabancin PDP.

Ta ce ana ganin Mark zai iya warware taƙaddamar PDP ne saboda yana kyakkyawar alaƙa da kowane ɓangaren a rigimar da ke faruwa a jam'iyyar.

Rikicin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike shi ne ya haifar da rarrabuwar kai a PDP a cewar rahoton Independent.

PDP ta ɗage taron NEC zuwa watan Nuwamba

A wani rahoton kuma jam'iyyar PDP mai adawa ta sake ɗage taron majalisar zartaswa na ƙasa (NEC) da ta shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Oktoban 2024.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ɗage taron zuwa Nuwamban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262