Minista Ya Shiga Matsala, An Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Kore Shi daga Aiki Nan Take
- Matasa sun buƙaci a kori ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu da shugaban kamfanin rarraba wuta na ƙasa TCN
- Ƙungiyar matasan NYTGG ta ce akwai sakaci a yawan lalacewar babban layin lantarki wanda ya samu matsala sau uku a mako guda
- A cewar kungiyar, rashin wuta ya jefa ƴan Najeeiya cikin duhu, ƴan kasuwar da ke amfani da lantarki sun tafka asara mai yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ga dukkan alamu rashin hasken wuta ya fara damun ƴan Najeriya yayin da wasu matasa suka roƙi a kori ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu.
Wata ƙungiyar matasan Najeriya (NYTGG) ta buƙaci a kori ministan wutar lantarki tare da shugaban kamfanin raba wuta TCN, Sule Ahmed Abdulaziz.
Meyasa aka nemi korar minista da shugaban TCN?
Matasan sun nemi a sallami waɗannan mutane biyu daga aiki ne saboda yawan katsewar babbar layin wuta na ƙasa a ƴan kwanakin nan, Leadership ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar matasa ta NYTGG, Abdullahi Sani ne ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kaduna.
Ya ce abubuwan da ke faruwa a ɓangaren samar da wutar lantarki da rarraba ta abin damuwa ne kuma kullum babu gyara sai ƙara taɓarɓarewa.
Abdullahi ya koka cewa rashin wuta ya jefa mutane da yawa a duhu, ƴan kasuwa sun yi asara sannan tattalin arzikin ƙasa ya samu koma baya.
A cewarsa, daga hawan Tinubu kan madafun iko zuwa yanzu, wutar lantarki ta lalace sau da dama wanda ya haddasa rashin hasken wuta a mafi yawan sassan ƙasar nan.
Rashin wuta: Matasa sun nemi a ɗauki mataki
A rahoton Daily Post, shugaban NYTGG ya ce:
"Duba da wannan muna kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya sunan Adebayo Adelabu a cikin wadanda za a sallama idan ya tashi garambawul a majalisar zartaswa."
"Ya zama dole a ɗauki tsattsauran mataki kan yawan lalacewar babban layin wutar lantarki, bai kamata a bar lamarin sakaka ba,"
TCN ya yi bayanin lalacewar wutar lantarki
A wani labarin kuma kamfanin TCN ya bayar da rahoton lalacewar wutar lantarki a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.
Manajan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya bayyana cewa wasu layukan wuta da ke kan tashar Ugwaji-Apir ne suka samu matsala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng