Atiku Abubakar Ya Jingine Siyasa, Ya Aika Saƙon Musamman Ga Kwankwaso

Atiku Abubakar Ya Jingine Siyasa, Ya Aika Saƙon Musamman Ga Kwankwaso

  • Atiku Abubakar ya tura sakon taya murna ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da yake bikin cika shekaru 68
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce Kwankwaso ya yi wa al'ummar Kano da ƙasa baki ɗaya aiki a muƙamai daban-daban da ya riƙe
  • Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na NNPP a zaɓen 2023 ya cika shekara 68 a duniya yau Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya taya jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso murnar cika shekara 68.

A yau Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2024, tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya cika shekara 68 da haihuwa kuma tuni aka fara taya shi murna.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya karya tarihin shekara 20, ya ƙarawa ƴan fansho alawus duk wata

Kwankwaso da Atiku.
"Allah karo shekaru masu albarka," Kwankwaso ya taya Kwankwaso murna Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Kwankwaso ya cika shekara 68

Tsohon gwamnan ya kaddamar da babban ɗakin taro a Jami'ar Skyline a wani ɓangare na murnar wannan rana, sannnan ya ba gwamnatin Kano kyautar makaranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa mai nagarta wanda ya yiwa mutanen Kano da Najeriya hidima.

Wazirin Adamawa ya kuma yi fatan alheri da ƙarin shekaru masu albarka ga tsohon gwamnan jihar Kano.

Atiku Abubakar ya tura saƙo ga Kwankwaso

"A madadin iyali na, ina taya ɗan uwana Engr. Rabiu Musa Kwankwaso murna cika shekaru 68 da haihuwa a duniya.
"Kwankwaso jagoran siyasa ne wanda ya yi wa mutanen jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya hidima a muƙamai daban-daban da ya riƙe."
"Ina masaa fatan karin shekaru masu albarka da kuma ci gaba da yi wa ƙasar nan hidima."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ba mutane mamaki, ya faɗi abin da ya fi so a ayyukan da ya yi a Kano

- Alhaji Atiku Abubakar.

Sakon Atiku na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya uban gidansa murnar karin shekara, inda ya ce ya ɗauki shekaru masu yawa tare da Kwankwaso.

Kwankwaso ya bada kyautar makaranta a Kano

A wani labarin jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da kyautar sabuwar makaranta ga gwamnatin Kano

An rahoto cewa Kwankwaso ya gina makarantar mai ajujuwa tara a garin Rikadawa a karamar hukumar Madobi da ke Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262