Tsohon Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Gindaya Sharadin Haɗa Kai a Zaben 2027
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar SDP, Adewole Adebayo ya ce dole a samu manufa ɗaya idan za a haɗe a zaɓen 2027
- Ya ce gwamnatin Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari sun isa zama misalin haɗaka ba tare da manufa ba sai kwaɗayin mulki
- Ɗan siyasar wanda yake da burin mulki ya ce zai shiga kawancen siyasa ne kaɗai idan ƴan Najeriya suka haɗa kansu a wuri ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan taƙarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 karƙashin inuwar jam'iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo ya gindaya sharaɗin haɗa maja gabanin zaɓen 2027.
Tsohon ɗan takarar ya bayyana cewa dole ne a yi taro na hankali kuma manufofi su haɗu kafin ya shiga kowane irin kawancen siyasa ko maja a zabe mai zuwa.
Adebayo ya ce ya gwammace ya ci gaba da zama a jam'iyyar adawa da ya shiga wata hadakar siyasa mara manufa don neman mulki, Leadership ta kawo labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Buhari da Tinubu sun isa zama misali'
Ya ce gwamnatin shugaban kasa, Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari kaɗai sun isa misalin illar da haɗa kawance yake da shi idan manufa ba ta zo ɗaya ba.
"Ya zama dole a yi tataunawa ta hankali, neman mulki ba hauka ba ne, kun ga abin da ya faru da Buhari, ga kuma abubuwan da suke faruwa a gwamnatin yanzu.
"Abu na farko da ya kamata a yi shi ne a samu manufa guda ɗaya, idan ka na son buɗe banki, ba zai yiwu ka yi haɗin guiwa da waɗanda ke burin sata a bankin ba.
"Burinmu mu haɗa kai da dukkan ƴan Najeriya, idan ku ka duba ƙuri'un da manyan ƴan takara uku na sahun gaɓa suka samu, za ku ga mutane kaɗan ne suka zaɓe su."
Adebayo ya buƙaci ƴan Najeriya su farka
Jigon siyasar ya ce kamata ya yi ƴan Najeriya musamman waɗanda ke cikin wahala a wannan mulki, su haɗa kai su yi wa kansu karatun ta natsu.
A cewar Prince Adebayo, lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su gane ƙarfin kuri'unsu kuma su san waɗanda ya dace su ba amanar ƙasarsu, rahoton Daily Trust.
Atiku ya maida martani ga Wike
A wani rahoton kuma kalaman da ministan birnin tarayya, Barista Nyesom Wike ya yi a wani taro a Fatakwal, jihar Ribas sun fusata Atiku Abubakar.
A wani martani da Atiku ya yi wa Wike, ya ce ba zai iya kaskantar da kansa ya koma kamar Wike ba wanda ya siyasantar da komai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng