Rikicin APC Ya Ƙara Kamari, Babban Basarake a Arewa Ya Yi Murabus daga Sarauta

Rikicin APC Ya Ƙara Kamari, Babban Basarake a Arewa Ya Yi Murabus daga Sarauta

  • Rikicin cikin gida da ya ɓarke a APC reshen jihar Sakkwato ya fara raba kawunan manyan jiga-jigai da sarakunan da ke taɓa siyasa
  • Hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa ya yi murabus daga sarauta saboda barin tsagin Sanata Wamakko
  • Jam'iyyar APC a Sakkwato ta dare gida biyu inda Sanata Aliyu Magatakardan Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido ke jagorantar kowane ɓangare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Hakimin Sabon Birni a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa, ya yi murabus daga sarauta.

Basaraken ya tabbatar da ajiye rawanin sarautar ne a wata wasiƙar murabus da ya aikawa na sama da shi mai ɗauke da kwanan watan 16 ga Oktoba, 2024.

Kara karanta wannan

An barke da murna da kamfanin NNPCL da Chevron suka sake hako wata rijiyar mai

Taswirar jihar Sokoto.
Hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa ya yi murabus Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Bawa shi ne sarkin gargajiya na farko da zuwa yanzu ya sanar da yin murabus tun bayan barkewar rikici a cikin APC mai mulki, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa hakimin ya yi murabus?

A takardar murabus ɗin hakimin Sabon Birni, ya ce:

"An naɗa ni a matsayin hakimin Sabon Birni a ranar 15 ga watan Yuli, 2014, kuma a yau, 16 ga watan Oktoba, 2024, ina sanar da ajiye wannan sarauta domin koma wa tsagin Sanata Ibrahim Lamido."

Rikicin cikin gida da ya fara bayyana kimanin makonni biyu da suka gabata, ya yi ƙamari ne tsakanin Sanata Ibrahim Lamido da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

Wamakko, wanda tsohon gwamnan jihar ne, ana yi masa kallon shi ne jagoran jam’iyyar APC a Sakkwato kuma ubangidan Gwamna Ahmed Aliyu.

Yadda APC ta dare gida biyu a Sakkwato

Kara karanta wannan

"Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe," Gwamna ya faɗi hanya 1 da za a yi maganin ƴan bindiga

Rikicin dai ya raba APC gida biyu inda Wamakko da Lamido ke jagorantar bangarorin.

Kakakin tsagin Lamido, Hon. Sani Yakubu Gudu, ɗan majalisa mai wakiltar Tangaza/Gudu ya ce kwamishinoni da hadiman Gwamna Aliyu na tare da Lamido.

Bugu da tsari tsagin Sanata Lamido ya yi barazanar kafa sabon shugabancin APC saboda zargin jam'iyyar na dab da rugujewa a hannun Wamakko da Gwamna Aliyu.

A yanzu dai wannan rikici ne ya jawo hakimin Sabon Birni ya yanke shawarar ajiye muƙaminsa domin komawa ɓangaren Sanata Lamido.

Gwamna Aliyu ya rage farashin abinci

A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Sokoto za ta ƙaddamar da shirin sayar da shinkafa da sauran kayan abinci a kan farashi mai rahusa.

Gwamnatin za ta siyar da kayan abincin ne waɗanda aka zaftare kaso 55% daga farashin da ake siyo su a kasuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262