NNPP na Fama da Rikici a Kano, Ganduje Ya Sake Yiwa Jam'iyyar Adawa Lahani

NNPP na Fama da Rikici a Kano, Ganduje Ya Sake Yiwa Jam'iyyar Adawa Lahani

  • A daidai lokacin da NNPP ke fama da rikici a jiharsa ta Kano, Abdullahi Ganduje ya kara yiwa ƴan adawa lahani a jihar Ekiti
  • Tsohuwar ƴar takarar gwamna a inuwar ADP da magoya bayanta akalla 7,000 sun sauya sheka zuwa APC a hukumance ranar Alhamis
  • Kemi Elebute-Halle ta ce sun yanke shawarin shiga APC saboda sun gamsu da manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja -Tsohuwar ‘yar takarar gwamna a inuwar jam’iyyar ADP a Ekiti, Kemi Elebute-Halle, tare da magoya bayanta sun sauya sheƙa zuwa APC a hukumance.

Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya tarbi Elebute-Halle da magoya bayanta a hedkwatar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja jiya Alhamis.

Kara karanta wannan

"Na cancanta," Sanatan APC ya bayyana shirinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027

Elebute-Halle ta koma APC.
Ganduje ya karbi tsohuwar yar takara gwamna da magoya bayanta da suka sauya sheka zuwa APC Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Dalilin sauya shekar Elebute-Halle zuwa APC

Punch ta ce da yake jawabi, tsohuwar mataimakiyar shugaban ADP ta ƙasa ta ce sun yanke dawowa APC ne saboda sun gamsu da salon mulkin Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce gyare-gyaren da shugaban Bola Ahmed Tinubu ya kawo daga hawansa mulki na ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo hankalinta ta shigo APC.

Ƴar siyasar ta kuma yabawa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji wanda a cewarta shi ne ya lallaɓata ta dawo jam'iyyar APC mai mulki.

Ƴar siyasar ta yabi gwamnan Ekiti

"Mun shigo APC ne domin mu ba shugaban ƙasa Bola Tinubu gudummuwa wajen cimma ajendarsa ta sabunta fata, kuma muna da yaƙinin tsare-tsarensa za su kai gaci.
"Bayan tattaunawa da gwamnan mu, na yanke hukuncin karshe na shiga APC ranar 7 ga watan Oktoba a wurin wani gangami a Ekiti. A wannan rana mata da maza sama da 7,000 suka shiga APC.

Kara karanta wannan

Barau ya sake sharewa APC hanyar lashe zabe a Kano, kusoshin NNPP sun sauya sheka

"Mafi akasarin waɗanda suka sauya sheƙa sun fito ne daga yankuna shida, ba wai ƴan ADP kaɗai ba ne, har da ƴan jam'iyyun APP, ADP, AD, SDP, LP, PPA da PDP.

Ganduje ya ce an zama ɗaya

Yayin da yake karbar masu sauya shekar, Ganduje ya yabawa Elebete-Halle da magoya bayanta bisa amincewa da APC da salon mulkin Tinubu.

Ganduje ya tabbatar masu da cewa sun zama ɗaya da kowa a APC kuma da su za a ci gaba da tafiyar da harkokin jam'iyyar.

Sanatan APC zai nemi takara a 2027

A wani rahoton kuma Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa yana da gogewar zama shugaban kasa idan jam'iyyar APC ta ba shi dama a 2027.

Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce a shirye yake ya nemi takara a 2027 idan Bola Tinubu ya haƙura da tazarce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262