"Har Yanzu Yana Jin Raɗaɗin 2023," Jigon PDP Ya Kwancewa Tsohon Gwamna Zani a Kasuwa

"Har Yanzu Yana Jin Raɗaɗin 2023," Jigon PDP Ya Kwancewa Tsohon Gwamna Zani a Kasuwa

  • Jigon PDP ya bayyana cewa har yanzun Nyesom Wike bai gama murmurewa daga kayen da ya sha a zaben fitar da gwani ba
  • Dele Momodu ya yi ikirarin Wike ya ɗauka babu makawa sai ya zama shugaban kasa a 2023 amma ya sha kaye a zaɓen gwani
  • Ana ganin dai Wike tare da gwamnonin G5 sun taka rawar gani matuka wajen rashin nasarar Atiku a zaben shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dele Momodu ya bayyana cewa har yanzu Nyesom Wike bai murmure daga kayen da ya sha zaben fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ba a 2022.

Idan ba ku manta ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ne ya samu nasara a zaɓen da kuri'u 371, ya tumurmusa Wike mai kuri'u 237.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun raba gardama, sun sanar da sahihin shugaban jam'iyya na ƙasa

Wike da Dele Momodu.
Dele Momodu ya bayyana cewa har yau Wike bai murmure daga kayen da ya sha a zaben fidda gwani ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike, Dele Momodu
Asali: Facebook

Yadda Nyesom Wike ya tada rigima a PDP

Bayan haka ne Wike da wasu gwamnonin PDP huɗu a wancan lokacin suka ɓalle, suka kafa tawagar G5, suka yaƙi Atiku a zaben shugaban ƙasa, The Cable ta tuno da zancen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ganin cewa gwamnonin G5 sun taka rawa wajen kayar da Atiku a zaɓen 2023, wanda daga bisani rikicin ya ƙara yaɗuwa a jam'iyyar PDP.

Da yake magana a wata hira da Arise TV, Momodu ya ce Wike ya ji takaici saboda ya kasa samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

'Abin da ya ba Wike haushi a jam'iyyar PDP'

"Abu na farko Wike ya ji zafin kayen da Atiku ya masa a zaben fidda gwani a 2022 kuma tun a wancan lokacin alamu sun nuna bai farfaɗo ba.
"A lokacin Wike ya ɗauka babu makawa zai samu tikitin takara kuma ya zama shugaban Najeriya shiyasa abin ya masa zafi.

Kara karanta wannan

'Za su hana Tinubu takara a 2027?' Kusa ya dura kan masu sukar Atiku

"Idan mutum ya rasa abu a rayuwa dole zai ji ba daɗi, ba zamu hana shi ba, to amma mun yi tsammanin komai zai wuce bayan ƴan watanni, abu ya ƙi karewa har yau."

- Dele Momodu.

Damagum: Gwamnonin PDP sun ɗauki matsaya

A wani labarin kuma, gwamnonin PDP sun dauki manyan matakai yayin da rikicin jam'iyyar ya kara ƙamari wanda ya kai ga an samu rabuwar kawuna.

An rahoto cewa gwamnonin sun amince Umar Damagum ya ci gaba da zama matsayin shugaba zuwa ranar 24 ga Oktobar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262